< Zabura 96 >

1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka. 2 Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana. 3 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane. 4 Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. 5 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai. 6 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa. 7 Ku ba wa Ubangiji, ya iyalan al’ummai ku ba wa Ubangiji ɗaukaka da kuma ƙarfi. 8 Ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku kawo sadaka ku kuma zo cikin filayen gidansa. 9 Ku bauta wa Ubangiji da darajar tsarkinsa; ku yi rawar jiki a gabansa, dukan duniya. 10 Ku faɗa cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki.” Duniya ta kahu daram, ba za a iya matsar da ita ba; zai yi wa mutane hukunci da gaskiya. 11 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa; 12 bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki; 13 za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa.

< Zabura 96 >