< Zabura 92 >

1 Zabura ce. Waƙa ce. Domin ranar Asabbaci. Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka, 2 don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare, 3 da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya. 4 Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka. 5 Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai! 6 Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba, 7 cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada. 8 Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada. 9 Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta. 10 Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina. 11 Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana. 12 Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon; 13 da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu. 14 Za su ci gaba da ba da’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar, 15 suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”

< Zabura 92 >