< Zabura 90 >

1 Addu’ar Musa Mutumin Allah. Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai. 2 Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne. 3 Ka komar da mutane zuwa ƙura, kana cewa, “Ku koma ƙura, ya ku’ya’yan mutane.” 4 Gama shekaru dubu a gabanka kamar kwana ɗaya ne da ya wuce, ko sa’a guda na dare. 5 Ka share mutane cikin barcin mutuwa; suna kama da sabuwa ciyawar safiya, 6 ko da yake da safe takan yi sabuwar huda da yamma sai ta bushe ta kuma yanƙwane. 7 An cinye mu ta wurin fushinka mun kuma razana ta wurin hasalarka. 8 Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka. 9 Dukan kwanakinmu sun wuce ƙarƙashin fushinka; mun gama shekarunmu da nishi. 10 Tsawon kwanakinmu shekaru saba’in ne, ko tamanin, in muna da ƙarfi; duk da haka tsawonsu wahaloli ne kawai da ɓacin rai, gama da sauri suke wucewa, ta mu kuma ta ƙare. 11 Wa ya san ƙarfin fushinka? Gama hasalarka tana da girma kamar tsoron da ya dace da kai. 12 Ka koya mana yawan kwanakinmu daidai, don mu sami zuciyar hikima. 13 Ka ji mu, ya Ubangiji! Har yaushe zai ci gaba? Ka ji tausayin bayinka. 14 Ka ƙosar da mu da safe da ƙaunarka marar ƙarewa, don mu rera don yabo, mu kuma yi murna dukan kwanakinmu. 15 Faranta mana zuciya kamar yawan kwanakin da muka sha azaba, kamar yawan shekarun da muka ga wahala. 16 Bari a nuna ayyukanka ga bayinka, darajarka ga’ya’yansu. 17 Bari alherin shugabanmu Allah yă kasance a kanmu; ka albarkaci mana aikin hannuwanmu, I, ka albarkaci aikin hannuwanmu.

< Zabura 90 >