< Zabura 88 >
1 Waƙa ce, Zabura ta’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannotmaskil na Heman dangin Ezra. Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.
2 Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata.
3 Gama raina yana cike da wahala rayuwata tana gab da kabari. (Sheol )
4 An lissafta ni cikin waɗanda suka gangara zuwa cikin rami; ni kamar mutumin da ba shi da ƙarfi ne.
5 An ware ni tare da matattu, kamar waɗanda aka kashe da suke kwance a kabari, waɗanda ba ka ƙara tunawa, waɗanda aka yanke daga taimakonka.
6 Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu.
7 Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka. (Sela)
8 Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta
9 idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.
10 Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne? (Sela)
11 Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?
12 An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?
13 Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.
14 Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?
15 Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.
16 Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.
17 Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.
18 Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.