< Zabura 84 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki! 2 Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai. 3 Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna. 4 Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. (Sela) 5 Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne. 6 Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna. 7 Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona. 8 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. (Sela) 9 Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka. 10 Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye. 11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai. 12 Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

< Zabura 84 >