< Zabura 76 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila. 2 Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona. 3 A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. (Sela) 4 Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa. 5 Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa. 6 A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi. 7 Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi? 8 Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit, 9 sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. (Sela) 10 Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka. 11 Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro. 12 Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.

< Zabura 76 >