< Zabura 67 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura. Waƙa. Bari Allah yă yi mana alheri yă kuma albarkace mu yă kuma sa fuskarsa ta haskaka a kanmu, (Sela) 2 don a san hanyoyinka a duniya, cetonka kuma a cikin dukan al’ummai. 3 Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka. 4 Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. (Sela) 5 Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe. 6 Sa’an nan ƙasa za tă ba da girbinta Allah kuma, Allahnmu, zai albarkace mu. 7 Allah yă sa mana albarka, dukan iyakar duniya kuma su ji tsoronsa.

< Zabura 67 >