< Zabura 66 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya! 2 Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka! 3 Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka. 4 Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” (Sela) 5 Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum! 6 Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa. 7 Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada’yan tawaye su tayar masa. (Sela) 8 Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa; 9 ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi. 10 Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa. 11 Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu. 12 Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa. 13 Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka, 14 alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala. 15 Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. (Sela) 16 Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini. 17 Na yi kuka gare shi da bakina; yabonsa yana a harshena. 18 Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba; 19 amma tabbatacce Allah ya saurara ya kuma ji muryata a cikin addu’a. 20 Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!

< Zabura 66 >