< Zabura 63 >

1 Zabura ta Dawuda. Sa’ad da yake a hamadar Yahuda. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. 2 Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. 3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. 4 Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. 5 Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. 6 A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. 7 Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. 8 Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni. 9 Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya. 10 Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji. 11 Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.

< Zabura 63 >