< Zabura 50 >

1 Zabura ta Asaf. Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa. 2 Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa. 3 Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi. 4 Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa. 5 “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.” 6 Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. (Sela) 7 “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku. 8 Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana. 9 Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku, 10 gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai. 11 Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne. 12 Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta. 13 Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne? 14 “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka, 15 ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.” 16 Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku? 17 Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku 18 Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata. 19 Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu. 20 Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku. 21 Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku. 22 “Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku. 23 Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”

< Zabura 50 >