< Zabura 47 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki. 2 Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! 3 Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. 4 Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. (Sela) 5 Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. 6 Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. 7 Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. 8 Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki. 9 Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.

< Zabura 47 >