< Zabura 150 >

1 Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa. 2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa. 3 Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo, 4 yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa, 5 yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai. 6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.

< Zabura 150 >