< Zabura 149 >

1 Yabi Ubangiji. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, yabonsa a cikin taron tsarkaka. 2 Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu. 3 Bari su yabi sunansa tare da rawa suna kuma yin kiɗi gare shi da ganga da garaya. 4 Gama Ubangiji yana jin daɗin mutanensa; yakan darjanta masu sauƙinkai da ceto. 5 Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu. 6 Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu, 7 don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane, 8 don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe, 9 don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.

< Zabura 149 >