< Zabura 146 >

1 Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina. 2 Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina. 3 Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto. 4 Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza. 5 Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa. 6 Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada. 7 Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan’yantar da’yan kurkuku, 8 Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci. 9 Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye. 10 Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji.

< Zabura 146 >