< Zabura 141 >

1 Zabura ta Dawuda. Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira. 2 Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma. 3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana. 4 Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu. 5 Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka. 6 Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne. 7 Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.” (Sheol h7585) 8 Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa. 9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa. 10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya.

< Zabura 141 >