< Zabura 138 >

1 Ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo. 2 Zan rusuna ta wajen haikalinka mai tsarki zan kuma yabi sunanka saboda ƙaunarka da amincinka, saboda ka ɗaukaka a bisa kome sunanka da kuma maganarka. 3 Sa’ad da na kira, ka amsa mini; ka sa na zama mai ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa ni. 4 Bari dukan sarakunan duniya su yabe ka, ya Ubangiji, sa’ad da suka ji maganganun bakinka. 5 Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take. 6 Ko da yake Ubangiji yana bisa, yakan dubi kāsassu, amma tun da nesa ya san masu girman kai. 7 Ko da na yi tafiya a tsakiyar wahala, kana kiyaye raina; ka miƙa hannunka a kan fushin maƙiyana, da hannunka na dama ka cece ni. 8 Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.

< Zabura 138 >