< Zabura 128 >

1 Waƙar haurawa. Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa. 2 Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka. 3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai’ya’ya a cikin gidanka;’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka. 4 Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji. 5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima, 6 bari kuma ka rayu ka ga’ya’ya’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

< Zabura 128 >