< Zabura 125 >

1 Waƙar haurawa. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona, wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada. 2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma. 3 Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance a kan ƙasar da take rabon adalai ba, domin kada masu adalci su yi amfani da hannuwansu su aikata mugunta. 4 Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu, ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu. 5 Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

< Zabura 125 >