< Zabura 124 >

1 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce, 2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana, 3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai; 4 da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu. 5 Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf. 6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba. 7 Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira. 8 Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.

< Zabura 124 >