< Zabura 12 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane. 2 Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu. 3 Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya, 4 masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?” 5 “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.” 6 Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai. 7 Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada. 8 Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.

< Zabura 12 >