< Zabura 113 >

1 Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji. 2 Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma. 3 Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji. 4 Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai 5 Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa, 6 wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya? 7 Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; 8 ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu. 9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji.

< Zabura 113 >