< Zabura 111 >

1 Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro. 2 Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu. 3 Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada. 4 Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma. 5 Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada. 6 Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai. 7 Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne. 8 Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya. 9 Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa. 10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo.

< Zabura 111 >