< Zabura 110 >

1 Ta Dawuda. Zabura ce. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” 2 Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka. 3 Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka. 4 Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” 5 Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa. 6 Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya. 7 Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama.

< Zabura 110 >