< Karin Magana 25 >

1 Waɗannan ƙarin karin maganar Solomon ne waɗanda mutanen Hezekiya sarkin Yahuda suka tara. 2 Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne. 3 Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika. 4 Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa; 5 ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci. 6 Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki, kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane; 7 gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka 8 kada ka yi garaje kai ƙara a majalisa, gama me za ka yi a ƙarshe in maƙwabcinka ya ba ka kunya? 9 In kai da maƙwabcinka kuka yi gardama, kada ka tona asirin wani, 10 in ba haka ba duk wanda ya ji zai kunyata ka ba za ka kuma taɓa rabuwa da wannan mummuna suna ba. 11 Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa. 12 Kamar’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa. 13 Kamar sanyin ƙanƙara a lokacin girbi haka ɗan saƙo mai aminci wanda aka aika; ya wartsakar da ran waɗanda suka aike shi. 14 Kamar gizagizai da kuma iska marar ruwan sama haka mutumin da yake fariya a kan kyautan da ba ya bayarwa. 15 Ta wurin haƙuri akan rinjaye mai mulki, magana mai hankali kan karye ƙashi. 16 In ka sami zuma, ka sha isashe kawai, in ya yi yawa, za ka yi amai. 17 Kada ka cika ziyarar gidan maƙwabcinka yawan ganinka zai sa ya ƙi ka. 18 Kamar sanda ko takobi ko kibiya mai tsini haka yake da mutumin da yake ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinsa. 19 Kamar haƙori mai ciwo ko yin tafiya da gurguwar ƙafa haka yake ga mai dogara da marasa aminci a lokacin wahala. 20 Kamar wanda ya tuɓe riga a ranar da ake sanyi, ko kuwa kamar zuba ruwan tsami a kanwa, haka yake da mai rera waƙoƙi ga mai baƙin ciki. 21 In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha. 22 Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka. 23 Kamar yadda iskar arewa kan kawo ruwan sama, haka jita-jita kan kawo fushi. 24 Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina. 25 Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa. 26 Kamar rafi mai laka ko rijiyar da ta gurɓace haka yake da mai adalci wanda ya miƙa wuya ga mugaye. 27 Ba shi da kyau ka sha zuma da yawa, haka ma ba shi da kyau ka nemi girma wa kanka. 28 Kamar birni da katangarsa sun rushe haka yake da mutumin da ba ya iya danne fushinsa.

< Karin Magana 25 >