< Ƙidaya 6 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
Yahweh spoke to Moses, saying,
2 “Yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘In mace, ko namiji yana so yă yi alkawari na musamman, alkawarin zaman keɓaɓɓe ga Ubangiji, a matsayin Banazare,
“Speak to the children of Israel, and tell them: ‘When either man or woman shall make a special vow, the vow of a Nazirite, to separate himself to Yahweh,
3 dole yă keɓe kansa daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye, kada kuma yă sha ruwan tsamin da aka yi daga ruwan inabi, ko daga waɗansu abubuwa sha masu sa maye. Ba zai sha ruwan’ya’yan inabi, ko yă ci’ya’yan inabi ɗanye ko busasshe ba.
he shall separate himself from wine and strong drink. He shall drink no vinegar of wine, or vinegar of fermented drink, neither shall he drink any juice of grapes, nor eat fresh grapes or dried.
4 Muddin yana Banazare, ba zai ci wani abin da ya fito daga’ya’yan inabi ba, ko ƙwayar inabi, ko ɓawonsa ma.
All the days of his separation he shall eat nothing that is made of the grapevine, from the seeds even to the skins.
5 “‘A dukan lokacin da yake a kan alkawarin keɓewarsa, reza ba zai taɓa kansa. Dole yă kasance da tsarki har ƙarshen keɓewarsa ga Ubangiji; tilas yă bar gashin kansa yă yi tsawo.
“‘All the days of his vow of separation no razor shall come on his head, until the days are fulfilled in which he separates himself to Yahweh. He shall be holy. He shall let the locks of the hair of his head grow long.
6 A dukan kwanakin keɓewarsa ga Ubangiji, Banazarin ba zai yi kusa da gawa ba.
“‘All the days that he separates himself to Yahweh he shall not go near a dead body.
7 Ko da ma gawar ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan mahaifiyarsa, ko kuma ta’yar’uwarsa ce, ba zai ƙazantar da kansa saboda su ba, domin alamar keɓewarsa ga Allah tana kansa.
He shall not make himself unclean for his father, or for his mother, for his brother, or for his sister, when they die, because his separation to God is on his head.
8 A dukan kwanakin keɓewarsa, an tsarkake shi ga Ubangiji.
All the days of his separation he is holy to Yahweh.
9 “‘In farat ɗaya wani ya mutu kusa da shi, to, keɓewarsa ta ƙazantu, dole yă aske kansa a ranar tsarkakewarsa, a rana ta bakwai.
“‘If any man dies very suddenly beside him, and he defiles the head of his separation, then he shall shave his head in the day of his cleansing. On the seventh day he shall shave it.
10 Sa’an nan a rana ta takwas, tilas yă kawo wa firist’yan kurciyoyi biyu, ko kuma’yan tattabarai biyu a bakin ƙofar Tentin Sujada.
On the eighth day he shall bring two turtledoves or two young pigeons to the priest, to the door of the Tent of Meeting.
11 Firist kuwa zai miƙa ɗaya don hadaya ta zunubi, ɗayan kuma don hadaya ta ƙonawa, yă yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi ta dalilin gawar. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.
The priest shall offer one for a sin offering, and the other for a burnt offering, and make atonement for him, because he sinned by reason of the dead, and shall make his head holy that same day.
12 Dole yă keɓe kansa ga Ubangiji, har kwanakin keɓewarsa, kuma dole yă kawo ɗan rago bana ɗaya a matsayin hadayar laifi. Kwanakin baya ba sa cikin lissafi, domin ya ƙazantu a lokacin keɓewarsa.
He shall separate to Yahweh the days of his separation, and shall bring a male lamb a year old for a trespass offering; but the former days shall be void, because his separation was defiled.
13 “‘To, ga doka saboda Banazare sa’ad da kwanakin keɓewarsa suka gama. Za a kawo shi a bakin ƙofar Tentin Sujada.
“‘This is the law of the Nazirite: when the days of his separation are fulfilled, he shall be brought to the door of the Tent of Meeting,
14 A can zai miƙa hadayunsa ga Ubangiji. Hadayun kuwa su ne, ɗan rago, bana ɗaya marar lahani don hadaya ta ƙonawa,’yar tunkiya, bana ɗaya marar lahani na hadaya don zunubi, rago marar lahani don hadaya ta salama,
and he shall offer his offering to Yahweh: one male lamb a year old without defect for a burnt offering, one ewe lamb a year old without defect for a sin offering, one ram without defect for peace offerings,
15 tare da hadayu na hatsi da hadayu na sha, da kuma kwando burodi marar yisti, ƙosai da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da kuma wainan da aka barbaɗa da mai.
a basket of unleavened bread, cakes of fine flour mixed with oil, and unleavened wafers anointed with oil with their meal offering and their drink offerings.
16 “‘Firist zai kawo su a gaban Ubangiji, yă miƙa hadaya don zunubi da hadaya ta ƙonawa.
The priest shall present them before Yahweh, and shall offer his sin offering and his burnt offering.
17 Zai miƙa kwandon burodi marar yisti, yă kuma miƙa ɗan ragon hadaya ta salama tare da hadaya ta gari, da hadaya ta sha ga Ubangiji.
He shall offer the ram for a sacrifice of peace offerings to Yahweh, with the basket of unleavened bread. The priest shall offer also its meal offering and its drink offering.
18 “‘Sa’an nan a ƙofar Tentin Sujada, dole Banazaren yă aske gashin da ya alamta keɓewarsa, yă kwashe gashin, yă zuba a cikin wutar da take ƙarƙashin hadaya ta salama.
The Nazirite shall shave the head of his separation at the door of the Tent of Meeting, take the hair of the head of his separation, and put it on the fire which is under the sacrifice of peace offerings.
19 “‘Bayan Banazaren ya aske gashinsa da ya alamta keɓewa, firist zai ɗauki dafaffiyar kafaɗar rago, da ƙosai da kuma waina daga cikin kwando waɗanda duka biyu marar yisti ne, yă sa su a tafin hannun keɓaɓɓen.
The priest shall take the boiled shoulder of the ram, one unleavened cake out of the basket, and one unleavened wafer, and shall put them on the hands of the Nazirite after he has shaved the head of his separation;
20 Firist zai kaɗa su a gaban Ubangiji, hadaya ce ta kaɗawa; mai tsarki ne kuma, zai zama na firist, tare da ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka kawo. Bayan haka, Banazaren zai iya shan ruwan inabi.
and the priest shall wave them for a wave offering before Yahweh. They are holy for the priest, together with the breast that is waved and the thigh that is offered. After that the Nazirite may drink wine.
21 “‘Wannan ita ce dokar Banazare wanda ya yi alkawari ga Ubangiji bisa ga keɓewarsa, tare da duk abin da zai iya bayarwa. Tilas yă cika alkawarin da ya yi bisa ga dokar zaman Banazare.’”
“‘This is the law of the Nazirite who vows and of his offering to Yahweh for his separation, in addition to that which he is able to afford. According to his vow which he vows, so he must do after the law of his separation.’”
22 Ubangiji ya ce wa Musa,
Yahweh spoke to Moses, saying,
23 “Gaya wa Haruna da’ya’yansa, ‘Ga yadda za ku albarkaci Isra’ilawa. Za ku ce musu,
“Speak to Aaron and to his sons, saying, ‘This is how you shall bless the children of Israel.’ You shall tell them,
24 “‘“Ubangiji yă albarkace ku, yă kuma kiyaye ku;
‘Yahweh bless you, and keep you.
25 Ubangiji yă sa fuskarsa ta haskaka a kanku, yă kuma yi muku alheri;
Yahweh make his face to shine on you, and be gracious to you.
26 Ubangiji yă dube ku da idon rahama, yă kuma ba ku salama.”’
Yahweh lift up his face toward you, and give you peace.’
27 “Da haka za su sa sunana a kan Isra’ilawa, ni kuma zan albarkace su.”
“So they shall put my name on the children of Israel; and I will bless them.”

< Ƙidaya 6 >