< Ƙidaya 29 >

1 “‘A rana ta farko ga wata na bakwai, a yi tsattsarkan taro, kada kuma a yi aikin da aka saba na kullum. Rana ce don busa ƙahoni.
「七月初一日,你們當有聖會;甚麼勞碌的工都不可做,是你們當守為吹角的日子。
2 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda,’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji, duka su kasance marasa lahani.
你們要將公牛犢一隻,公綿羊一隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔七隻,作為馨香的燔祭獻給耶和華。
3 Tare da bijimin za a kuma miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai;
同獻的素祭用調油的細麵;為一隻公牛要獻伊法十分之三;為一隻公羊要獻伊法十分之二;
4 kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
為那七隻羊羔,每隻要獻伊法十分之一。
5 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara.
又獻一隻公山羊作贖罪祭,為你們贖罪。
6 Waɗannan ƙari ne ga hadayun ƙonawa na wata-wata da na kullayaumi, tare da hadayun garinsu da hadayun sha yadda aka tsara. Hadayu ne da aka miƙa wa Ubangiji ta wuta don daɗin ƙanshi.
這些是在月朔的燔祭和同獻的素祭,並常獻的燔祭與同獻的素祭,以及照例同獻的奠祭以外,都作為馨香的火祭獻給耶和華。」
7 “‘A rana ta goma ga wannan watan bakwai, za a yi tsattsarkan taro. Ba za ku ci abinci ba, ba kuma za ku yi aiki ba.
「七月初十日,你們當有聖會;要刻苦己心,甚麼工都不可做。
8 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da kuma’yan raguna bakwai,’yan bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
只要將公牛犢一隻,公綿羊一隻,一歲的公羊羔七隻,都要沒有殘疾的,作為馨香的燔祭獻給耶和華。
9 Tare da bijimin a miƙa hadaya ta gari na kashi ɗaya bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai; da rago guda, kashi biyu bisa goma na efa, na lallausan gari kwaɓaɓɓe, da mai;
同獻的素祭用調油的細麵:為一隻公牛要獻伊法十分之三;為一隻公羊要獻伊法十分之二;
10 kowane’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.
為那七隻羊羔,每隻要獻伊法十分之一。
11 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu.
又獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在贖罪祭和常獻的燔祭,與同獻的素祭並同獻的奠祭以外。」
12 “‘A rana ta goma sha biyar ga wata na bakwai, za a yi tsattsarkan taro, ba kuwa za a yi aikin da aka saba yi ba. Ku yi biki ga Ubangiji har kwana bakwai.
「七月十五日,你們當有聖會;甚麼勞碌的工都不可做,要向耶和華守節七日。
13 A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
又要將公牛犢十三隻,公綿羊兩隻,一歲的公羊羔十四隻,都要沒有殘疾的,用火獻給耶和華為馨香的燔祭。
14 Da kowane bijimai goma sha uku nan, a miƙa hadaya ta gari, kashi uku bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai; da ragunan biyu ɗin, a miƙa hadaya ta gari kashi biyu bisa goma na efa, kwaɓaɓɓe da mai;
同獻的素祭用調油的細麵;為那十三隻公牛,每隻要獻伊法十分之三;為那兩隻公羊,每隻要獻伊法十分之二;
15 tare kuma da kowane’yan raguna goma sha huɗu, kashi ɗaya bisa goma.
為那十四隻羊羔,每隻要獻伊法十分之一。
16 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa na kullum tare da hadayarta, ta gari da kuma hadaya ta sha.
並獻一隻公山羊為贖罪祭,這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
17 “‘A rana ta biyu, a miƙa bijimai goma sha biyu, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
「第二日要獻公牛犢十二隻,公綿羊兩隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔十四隻;
18 Tare da bijiman, ragunan da’yan ragunan a miƙa hadayarsu da gari da hadaya ta sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
並為公牛、公羊,和羊羔,按數照例,獻同獻的素祭和同獻的奠祭。
19 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya, don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadayunsu ta sha.
又要獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
20 “‘A rana ta uku za a miƙa bijimai goma sha ɗaya, raguna biyu, da kuma’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
「第三日要獻公牛十一隻,公羊兩隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔十四隻;
21 Tare da bijiman, ragunan da’yan raguna, a miƙa hadayun gari da hadayun sha, bisa ga adadin da aka ƙayyade.
並為公牛、公羊,和羊羔,按數照例,獻同獻的素祭和同獻的奠祭。
22 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
又要獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
23 “‘A rana ta huɗu a miƙa bijimai goma, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
「第四日要獻公牛十隻,公羊兩隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔十四隻;
24 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
並為公牛、公羊,和羊羔,按數照例,獻同獻的素祭和同獻的奠祭。
25 A haɗa da bunsuru guda, a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
又要獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
26 “‘A rana ta biyar a miƙa bijimai tara, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
「第五日要獻公牛九隻,公羊兩隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔十四隻;
27 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan ragunan, a miƙa hadayu na gari, da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
並為公牛、公羊,和羊羔,按數照例,獻同獻的素祭和同獻的奠祭。
28 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gari da hadaya ta sha.
又要獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
29 “‘A rana ta shida a miƙa bijimai takwas, raguna biyu, da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
「第六日要獻公牛八隻,公羊兩隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔十四隻;
30 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu ta gari da hadayu na sha bisa adadin da a ƙayyade.
並為公牛、公羊,和羊羔,按數照例,獻同獻的素祭和同獻的奠祭。
31 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadaya ta sha.
又要獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
32 “‘A rana ta bakwai a miƙa bijimai bakwai, raguna biyu da’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
「第七日要獻公牛七隻,公羊兩隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔十四隻;
33 Tare da bijiman, ragunan da kuma’yan raguna, a miƙa hadayunsu na gari, da hadayun sha bisa ga adadin da a ƙayyade.
並為公牛、公羊,和羊羔,按數照例,獻同獻的素祭和同獻的奠祭。
34 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
又要獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
35 “‘A rana ta takwas kuwa za a yi tsattsarkan taro, ban da aikin da aka saba.
「第八日你們當有嚴肅會;甚麼勞碌的工都不可做;
36 A miƙa hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, a yi hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, rago guda, da’yan raguna bakwai, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
只要將公牛一隻,公羊一隻,沒有殘疾、一歲的公羊羔七隻作火祭,獻給耶和華為馨香的燔祭;
37 Tare da bijimin, ragon da kuma’yan ragunan, a miƙa hadayunsu na gari da hadayu na sha bisa ga adadin da aka ƙayyade.
並為公牛、公羊,和羊羔,按數照例,獻同獻的素祭和同獻的奠祭。
38 A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, ban da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta hatsi da hadayarta ta sha.
又要獻一隻公山羊為贖罪祭。這是在常獻的燔祭和同獻的素祭並同獻的奠祭以外。
39 “‘Ban da abin da kuka yi alkawari, da kuma sadakokinku na yardar rai, a miƙa waɗannan ga Ubangiji a lokacin bukukkuwanku, hadayunku na ƙonawa, hadayu na gari, hadayu na sha da hadayu na salama.’”
「這些祭要在你們的節期獻給耶和華,都在所許的願並甘心所獻的以外,作為你們的燔祭、素祭、奠祭,和平安祭。」
40 Musa ya faɗa wa Isra’ilawa dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.
於是,摩西照耶和華所吩咐他的一切話告訴以色列人。

< Ƙidaya 29 >