< Malaki 4 >

1 “Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. 2 Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar’yan maruƙan da aka sake daga garke. 3 Sa’an nan za ku tattake mugaye; za su zama toka a ƙarƙashin tafin ƙafafunku a ranar da zan aikata waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji Maɗaukaki. 4 “Ku tuna da dokar bawana Musa, ƙa’idodi da dokokin da na ba shi a Horeb domin dukan Isra’ila. 5 “Ga shi, zan aika muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji tă zo. 6 Zai juye zukatan iyaye ga’ya’yansu, zukatan’ya’ya kuma ga iyayensu; in ba haka ba zan bugi ƙasar da hallaka gaba ɗaya.”

< Malaki 4 >