< Mahukunta 10 >

1 Bayan zamanin Abimelek, sai Tola ɗan Fuwa ɗan Dodo daga Issakar ya tashi don yă ceci Isra’ila. Yana zama a Shamir a ƙasar tudu ta Efraim. 2 Ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da uku sa’an nan ya mutu, aka kuma binne shi a Shamir. 3 Bayansa kuma sai Yayir daga Gileyad, wanda ya shugabanci Isra’ila shekara ashirin da biyu. 4 Yana’ya’ya talatin, waɗanda suke hawan jakuna talatin. Sun shugabanci birane talatin a Gileyad, har wa yau ana ce da biranen Hawwot Yayir. 5 Sa’ad da Yayir ya mutu, sai aka binne shi a Kamon. 6 Isra’ilawa suka sāke yin mugayen ayyuka a gaban Ubangiji. Suka shiga bautar Ba’al da Ashtarot, da kuma allolin Aram, allolin Sidon, allolin Mowab, Ammonawa da kuma allolin Filistiyawa. Kuma domin Isra’ilawa sun bar Ubangiji ba su ƙara bauta masa ba, 7 sai ya fusata da su. Ya sayar da su ga hannun Filistiyawa da Ammonawa, 8 waɗanda suka fatattake su a shekarar suka kuma ragargaza su. Shekara goma sha takwas suka yi ta danne dukan Isra’ilawan da suke gabashin Urdun a Gileyad, ƙasar Amoriyawa. 9 Ammonawa su ma suka haye Urdun domin su yi yaƙi da Yahuda, Benyamin da kuma gidan Efraim; Isra’ila kuwa suka kasance cikin wahala ƙwarai da gaske. 10 Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.” 11 Ubangiji ya ce, “Sa’ad da Masarawa, Amoriyawa, Ammonawa, Filistiyawa, 12 Sidoniyawa, Amalekawa da kuma mutanen Mawon suka wulaƙanta ku kuka kuwa yi mini kuka, ban cece ku daga hannunsu ba? 13 Amma kuka bar ni kuka bauta wa waɗansu alloli, saboda haka ni ma ba zan ƙara cece ku ba. 14 Ku tafi ku yi wa allolin da kuka zaɓa. Bari su cece ku sa’ad da kuke cikin wahala!” 15 Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.” 16 Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba. 17 Sa’ad da aka kira Ammonawa su yi ɗamarar yaƙi, sai su kuma kafa sansani a Gileyad, Isra’ilawa kuwa suka tattaru suka kafa sansani Mizfa. 18 Shugabannin mutanen Gileyad suka cewa juna, “Duk wanda zai fara fāɗa wa Ammonawa shi zai zama shugaban duk waɗanda suke zama a Gileyad.”

< Mahukunta 10 >