< Ayuba 5 >

1 “Ka yi kira in kana so, amma wa zai amsa maka? Wurin waɗanne tsarkaka za ka juya? 2 Fushi yana kashe wawa, ƙyashi kuma yana kashe marar azanci. 3 Ni ma na ga wawa yana cin gaba, amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne. 4 ’Ya’yansa suna cikin hatsari, ba wanda zai tsaya musu a gaban alƙali, 5 mayunwata sun kwashe girbinsa, har abubuwan da suke cikin ƙaya, masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa. 6 Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa. 7 Duk da haka an haifi mutum don wahala ne, kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi. 8 “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata. 9 Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa. 10 Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki. 11 Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki. 12 Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi. 13 Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba. 14 Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke. 15 Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi. 16 Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru. 17 “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki. 18 Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi. 19 Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka. 20 Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi. 21 Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo. 22 Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya; kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji. 23 Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai. 24 Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka, za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan. 25 Za ka san cewa’ya’yanka za su zama da yawa, zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa. 26 Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi. 27 “Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.”

< Ayuba 5 >