< Irmiya 23 >

1 “Kaiton makiyayan da suka hallakar suka kuma warwatsar da tumakin makiyayanta!” In ji Ubangiji.
הוי רעים מאבדים ומפצים את צאן מרעיתי--נאם יהוה
2 Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana ce wa makiyayan da suke lura da mutanena, “Domin kun watsar da garkena kuka kuma kore su ba ku kuma lura da su ba, zan kawo hukunci a kanku saboda muguntar da kuka yi,” in ji Ubangiji.
לכן כה אמר יהוה אלהי ישראל על הרעים הרעים את עמי אתם הפצתם את צאני ותדחום ולא פקדתם אתם הנני פקד עליכם את רע מעלליכם נאם יהוה
3 “Ni kaina zan tattara raguwar garkena daga ƙasashen da na kore su zuwa zan kuma dawo da su ga makiyayansu, inda za su yi ta haihuwa su riɓaɓɓanya.
ואני אקבץ את שארית צאני מכל הארצות אשר הדחתי אתם שם והשבתי אתהן על נוהן ופרו ורבו
4 Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji.
והקמתי עליהם רעים ורעום ולא ייראו עוד ולא יחתו ולא יפקדו נאם יהוה
5 “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci, Sarki wanda zai yi mulki da hikima ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.
הנה ימים באים נאם יהוה והקמתי לדוד צמח צדיק ומלך מלך והשכיל ועשה משפט וצדקה בארץ
6 A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda Isra’ila kuma zai zauna lafiya. Sunan da za a kira shi ke nan, Ubangiji Adalcinmu.
בימיו תושע יהודה וישראל ישכן לבטח וזה שמו אשר יקראו יהוה צדקנו
7 “Saboda haka fa, kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da mutanen ba za su ƙara cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da Isra’ila daga Masar ba,’
לכן הנה ימים באים נאם יהוה ולא יאמרו עוד חי יהוה אשר העלה את בני ישראל מארץ מצרים
8 amma za su ce, ‘Muddin Ubangiji yana raye, wanda ya fito da zuriyar Isra’ila daga ƙasar arewa da kuma daga dukan ƙasashen da ya yashe su.’ Sa’an nan za su zauna a ƙasarsu.”
כי אם חי יהוה אשר העלה ואשר הביא את זרע בית ישראל מארץ צפונה ומכל הארצות אשר הדחתים שם וישבו על אדמתם
9 Game da annabawa kuwa, Zuciyata ta karai; dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa. Na zama kamar wanda ya bugu, kamar mutumin da ruwan inabi ya sha kansa, saboda Ubangiji da kuma maganarsa mai tsarki.
לנבאים נשבר לבי בקרבי רחפו כל עצמותי--הייתי כאיש שכור וכגבר עברו יין מפני יהוה ומפני דברי קדשו
10 Ƙasar ta cika da mazinata; saboda la’ana ƙasar ta zama kango makiyaya a hamada ta bushe. Annabawa suna bin mugayen muradu suna kuma amfani da ƙarfinsu a hanyar marar kyau.
כי מנאפים מלאה הארץ--כי מפני אלה אבלה הארץ יבשו נאות מדבר ותהי מרוצתם רעה וגבורתם לא כן
11 “Annabi da firist dukansu biyu marasa sanin Allah ne; har ma a cikin haikalina na tarar da muguntarsu,” in ji Ubangiji.
כי גם נביא גם כהן חנפו גם בביתי מצאתי רעתם נאם יהוה
12 “Saboda haka hanyarsu za tă yi santsi; za a jefar da su cikin duhu a can kuwa za su fāɗi. Zan kawo musu masifa a shekarar da za a hukunta su,” in ji Ubangiji.
לכן יהיה דרכם להם כחלקלקות באפלה ידחו ונפלו בה כי אביא עליהם רעה שנת פקדתם נאם יהוה
13 “A cikin annabawan Samariya na ga wannan abin banƙyama. Suna annabci ta wurin Ba’al suna ɓad da mutanena Isra’ila.
ובנביאי שמרון ראיתי תפלה הנבאו בבעל ויתעו את עמי את ישראל
14 A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”
ובנבאי ירושלם ראיתי שערורה נאוף והלך בשקר וחזקו ידי מרעים לבלתי שבו איש מרעתו היו לי כלם כסדם וישביה כעמרה
15 Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa, “Zan sa su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwa mai dafi, domin daga annabawan Urushalima rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.”
לכן כה אמר יהוה צבאות על הנבאים הנני מאכיל אותם לענה והשקתים מי ראש כי מאת נביאי ירושלם יצאה חנפה לכל הארץ
16 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci; suna cika ku da sa zuciyar ƙarya. Suna maganar wahayi daga tunaninsu, ba daga bakin Ubangiji ba.
כה אמר יהוה צבאות אל תשמעו על דברי הנבאים הנבאים לכם--מהבלים המה אתכם חזון לבם ידברו לא מפי יהוה
17 Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni, ‘Ubangiji ya ce za ku zauna lafiya.’ Ga duka waɗanda suke bin taurin zukatansu kuwa sukan ce, ‘Babu lahanin da zai same ku.’
אמרים אמור למנאצי דבר יהוה שלום יהיה לכם וכל הלך בשררות לבו אמרו לא תבוא עליכם רעה
18 Amma wane ne a cikinsu ya taɓa tsaya a majalisar Ubangiji yă ga ko ya ji maganarsa? Wa ya saurari ya kuma ji maganarsa?
כי מי עמד בסוד יהוה וירא וישמע את דברו מי הקשיב דברי (דברו) וישמע
19 Ga shi, hadarin Ubangiji zai taso cikin hasala guguwa tana kaɗawa a kan kawunan mugaye.
הנה סערת יהוה חמה יצאה וסער מתחולל על ראש רשעים יחול
20 Fushin Ubangiji ba zai kau ba sai ya aikata nufin zuciyarsa. A kwanakin masu zuwa za ku gane sarai.
לא ישוב אף יהוה עד עשתו ועד הקימו מזמות לבו באחרית הימים תתבוננו בה בינה
21 Ban aiki waɗannan annabawa ba, duk da haka sun tafi da saƙonsu; ban yi musu magana ba, duk da haka sun yi annabci.
לא שלחתי את הנבאים והם רצו לא דברתי אליהם והם נבאו
22 Amma da a ce sun tsaya a majalisata, da sun yi shelar maganata ga mutanena sun kuma juyar da su daga mugayen hanyoyinsu da kuma daga mugayen ayyukansu.
ואם עמדו בסודי--וישמעו דברי את עמי וישבום מדרכם הרע ומרע מעלליהם
23 “Ni ɗin Allah na kusa ne kawai,” in ji Ubangiji, “ba Allah na nesa ba?
האלהי מקרב אני נאם יהוה ולא אלהי מרחק
24 Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?” In ji Ubangiji “Ban cika sama da ƙasa ba?” In ji Ubangiji.
אם יסתר איש במסתרים ואני לא אראנו נאם יהוה הלוא את השמים ואת הארץ אני מלא נאם יהוה
25 “Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’
שמעתי את אשר אמרו הנבאים הנבאים בשמי שקר לאמר חלמתי חלמתי
26 Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu?
עד מתי היש בלב הנבאים--נבאי השקר ונביאי תרמת לבם
27 Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada.
החשבים להשכיח את עמי שמי בחלומתם אשר יספרו איש לרעהו--כאשר שכחו אבותם את שמי בבעל
28 Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji.
הנביא אשר אתו חלום יספר חלום ואשר דברי אתו ידבר דברי אמת מה לתבן את הבר נאם יהוה
29 “Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?
הלוא כה דברי כאש נאם יהוה וכפטיש יפצץ סלע
30 “Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna.
לכן הנני על הנבאים נאם יהוה מגנבי דברי איש מאת רעהו
31 I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya furta.’
הנני על הנביאם נאם יהוה הלקחים לשונם וינאמו נאם
32 Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.
הנני על נבאי חלמות שקר נאם יהוה ויספרום ויתעו את עמי בשקריהם ובפחזותם ואנכי לא שלחתים ולא צויתים והועיל לא יועילו לעם הזה--נאם יהוה
33 “Sa’ad da waɗannan mutane, ko annabi ko firist, ya tambaye ka, ‘Mece ce maganarUbangiji?’ Ka ce musu, ‘Wace magana? Zan yashe ku, in ji Ubangiji.’
וכי ישאלך העם הזה או הנביא או כהן לאמר מה משא יהוה--ואמרת אליהם את מה משא ונטשתי אתכם נאם יהוה
34 In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa.
והנביא והכהן והעם אשר יאמר משא יהוה--ופקדתי על האיש ההוא ועל ביתו
35 Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’
כה תאמרו איש על רעהו ואיש אל אחיו מה ענה יהוה ומה דבר יהוה
36 Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu.
ומשא יהוה לא תזכרו עוד כי המשא יהיה לאיש דברו והפכתם את דברי אלהים חיים יהוה צבאות אלהינו
37 Ga abin da za ku ci gaba da faɗa wa annabi, ‘Mece ce amsar Ubangiji gare ka?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’
כה תאמר אל הנביא מה ענך יהוה ומה דבר יהוה
38 Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’
ואם משא יהוה תאמרו לכן כה אמר יהוה יען אמרכם את הדבר הזה משא יהוה--ואשלח אליכם לאמר לא תאמרו משא יהוה
39 Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku.
לכן הנני ונשיתי אתכם נשא ונטשתי אתכם ואת העיר אשר נתתי לכם ולאבותיכם--מעל פני
40 Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.”
ונתתי עליכם חרפת עולם וכלמות עולם אשר לא תשכח

< Irmiya 23 >