< Ishaya 2 >

1 Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima. 2 A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi. 3 Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima. 4 Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi. 5 Ki zo, ya gidan Yaƙub, bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji. 6 Ka rabu da mutanenka, gidan Yaƙub. Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas; suna yin duba kamar Filistiyawa suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah. 7 Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya; dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da dawakai; kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka. 8 Ƙasarsu ta cika da gumaka; sukan rusuna ga aikin hannuwansu, ga abin da yatsotsinsu suka yi. 9 Saboda an jawo mutum ƙasa aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam, kada ku gafarta musu. 10 Ku tafi cikin duwatsu, ku ɓuya cikin ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa! 11 Za a ƙasƙantar da mai girman kai za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana. 12 Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye domin dukan masu girman kai da masu fariya domin dukan waɗanda aka ɗaukaka (zai kuwa ƙasƙantar da su), 13 domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya, da kuma dukan itatuwan oak na Bashan, 14 domin dukan dogayen duwatsu da kuma tuddai masu tsayi, 15 domin kowace doguwar hasumiya da kowace katanga mai ƙarfi, 16 domin kowane jirgin ruwan kasuwanci da kuma jirgi mafi girma mafi kyau. 17 Za a jawo mai girman kai ƙasa a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana, 18 za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf. 19 Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya. 20 A wannan rana mutane za su zubar wa jaba da jamage gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya da suka yi don su bauta musu. 21 Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma zuwa tsagaggun duwatsu daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya. 22 Ku daina dogara ga mutum, wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa. Wace daraja gare shi?

< Ishaya 2 >