< Ishaya 15 >

1 Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne, An lalatar da Ar a Mowab, an hallaka ta da dare! An lalatar da Kir a Mowab, an hallaka ta da dare! 2 Dibon ya haura zuwa haikalinta, zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka; Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba. An aske kowane kai an kuma yanke kowane gemu. 3 A tituna sun sa tsummoki a jikunansu; a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa dukansu sai makoki suke yi, sun kwanta suna kuka. 4 Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi, aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz. Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi, har zuciyarsu ta karai. 5 Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab; mutanenta sun gudu har zuwa Zowar, har zuwa Eglat Shelishiya. Sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka; a kan hanyar zuwa Horonayim suna makoki saboda hallakawarsu. 6 Ruwayen Nimrim sun ƙafe ciyayin kuma sun bushe; tsire-tsire duk sun ɓace babu sauran ɗanyen abu. 7 Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su. 8 Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab; kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim, makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim. 9 Ruwayen Dimon sun cika da jini, amma zan yi ƙari a kan Dimon, zan kawo zaki a kan masu gudu na Mowab da kuma a kan waɗanda suka ragu a ƙasar.

< Ishaya 15 >