< Ishaya 12 >

1 A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni. 2 Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.” 3 Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto. 4 A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne. 5 Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya. 6 Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”

< Ishaya 12 >