< Farawa 36 >

1 Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).
エサウ、すなわちエドムの系図は次のとおりである。
2 Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye
エサウはカナンの娘たちのうちから妻をめとった。すなわちヘテびとエロンの娘アダと、ヒビびとヂベオンの子アナの娘アホリバマとである。
3 ya kuma auri Basemat’yar Ishmayel wadda take’yar’uwar Nebayiwot.
また、イシマエルの娘ネバヨテの妹バスマテをめとった。
4 Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.
アダはエリパズをエサウに産み、バスマテはリウエルを産み、
5 Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.
アホリバマはエウシ、ヤラム、コラを産んだ。これらはエサウの子であって、カナンの地で彼に生れた者である。
6 Isuwa ya ɗauki matansa da’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.
エサウは妻と子と娘と家のすべての人、家畜とすべての獣、またカナンの地で獲たすべての財産を携え、兄弟ヤコブを離れてほかの地へ行った。
7 Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu.
彼らの財産が多くて、一緒にいることができなかったからである。すなわち彼らが寄留した地は彼らの家畜のゆえに、彼らをささえることができなかったのである。
8 Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.
こうしてエサウはセイルの山地に住んだ。エサウはすなわちエドムである。
9 Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.
セイルの山地におったエドムびとの先祖エサウの系図は次のとおりである。
10 Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Isuwa maza, Elifaz, ɗan Ada matar Isuwa, da Reyuwel ɗan Basemat matar Isuwa.
エサウの子らの名は次のとおりである。すなわちエサウの妻アダの子はエリパズ。エサウの妻バスマテの子はリウエル。
11 ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
エリパズの子らはテマン、オマル、ゼポ、ガタム、ケナズである。
12 Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.
テムナはエサウの子エリパズのそばめで、アマレクをエリパズに産んだ。これらはエサウの妻アダの子らである。
13 ’Ya’yan Reyuwel maza su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
リウエルの子らは次のとおりである。すなわちナハテ、ゼラ、シャンマ、ミザであって、これらはエサウの妻バスマテの子らである。
14 ’Ya’yan Oholibama maza’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne, Yewush, Yalam da Kora.
ヂベオンの子アナの娘で、エサウの妻アホリバマの子らは次のとおりである。すなわち彼女はエウシ、ヤラム、コラをエサウに産んだ。
15 Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa,’Ya’ya Elifaz maza ɗan farin Isuwa, Shugabannin su ne; Teman, Omar, Zefo, Kenaz,
エサウの子らの中で、族長たる者は次のとおりである。すなわちエサウの長子エリパズの子らはテマンの族長、オマルの族長、ゼポの族長、ケナズの族長、
16 Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.
コラの族長、ガタムの族長、アマレクの族長である。これらはエリパズから出た族長で、エドムの地におった。これらはアダの子らである。
17 ’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.
エサウの子リウエルの子らは次のとおりである。すなわちナハテの族長、ゼラの族長、シャンマの族長、ミザの族長。これらはリウエルから出た族長で、エドムの地におった。これらはエサウの妻バスマテの子らである。
18 ’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa, Shugabannin su ne; Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Oholibama’yar Ana matar Isuwa.
エサウの妻アホリバマの子らは次のとおりである。すなわちエウシの族長、ヤラムの族長、コラの族長。これらはアナの娘で、エサウの妻アホリバマから出た族長である。
19 Waɗannan su ne’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.
これらはエサウすなわちエドムの子らで、族長たる者である。
20 Waɗannan su ne’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,
この地の住民ホリびとセイルの子らは次のとおりである。すなわちロタン、ショバル、ヂベオン、アナ、
21 Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa,’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.
デション、エゼル、デシャン。これらはセイルの子ホリびとから出た族長で、エドムの地におった。
22 ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna’yar’uwar Lotan ce.
ロタンの子らはホリ、ヘマムであり、ロタンの妹はテムナであった。
23 ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.
ショバルの子らは次のとおりである。すなわちアルワン、マナハテ、エバル、シポ、オナム。
24 ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. Wannan shi ne Ana wanda ya sami maɓulɓulan ruwan zafi a hamada yayinda yake kiwon jakuna na mahaifinsa Zibeyon.
ヂベオンの子らは次のとおりである。すなわちアヤとアナ。このアナは父ヂベオンのろばを飼っていた時、荒野で温泉を発見した者である。
25 ’Ya’yan Ana su ne, Dishon da Oholibama’yar Ana.
アナの子らは次のとおりである。すなわちデションとアホリバマ。アホリバマはアナの娘である。
26 ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.
デションの子らは次のとおりである。すなわちヘムダン、エシバン、イテラン、ケラン。
27 ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Akan.
エゼルの子らは次のとおりである。すなわちビルハン、ザワン、アカン。
28 ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.
デシャンの子らは次のとおりである。すなわちウズとアラン。
29 Waɗannan su ne manyan Horiyawa, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana,
ホリびとから出た族長は次のとおりである。すなわちロタンの族長、ショバルの族長、ヂベオンの族長、アナの族長、
30 Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, bisa ga ɓangarorinsu, a ƙasar Seyir.
デションの族長、エゼルの族長、デシャンの族長。これらはホリびとから出た族長であって、その氏族に従ってセイルの地におった者である。
31 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,
イスラエルの人々を治める王がまだなかった時、エドムの地を治めた王たちは次のとおりである。
32 Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.
ベオルの子ベラはエドムを治め、その都の名はデナバであった。
33 Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.
ベラが死んで、ボズラのゼラの子ヨバブがこれに代って王となった。
34 Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.
ヨバブが死んで、テマンびとの地のホシャムがこれに代って王となった。
35 Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.
ホシャムが死んで、ベダデの子ハダデがこれに代って王となった。彼はモアブの野でミデアンを撃った者である。その都の名はアビテであった。
36 Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.
ハダデが死んで、マスレカのサムラがこれに代って王となった。
37 Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi ya gāje shi.
サムラが死んでユフラテ川のほとりにあるレホボテのサウルがこれに代って王となった。
38 Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.
サウルが死んでアクボルの子バアル・ハナンがこれに代って王となった。
39 Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.
アクボルの子バアル・ハナンが死んで、ハダルがこれに代って王となった。その都の名はパウであった。その妻の名はメヘタベルといって、メザハブの娘マテレデの娘であった。
40 Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne, Timna, Alwa, Yetet.
エサウから出た族長の名は、その氏族と住所と名に従って言えば次のとおりである。すなわちテムナの族長、アルワの族長、エテテの族長、
41 Oholibama, Ela, Finon.
アホリバマの族長、エラの族長、ピノンの族長、
42 Kenaz, Teman, Mibzar.
ケナズの族長、テマンの族長、ミブザルの族長、
43 Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.
マグデエルの族長、イラムの族長。これらはエドムの族長たちであって、その領地内の住所に従っていったものである。エドムびとの先祖はエサウである。

< Farawa 36 >