< Farawa 34 >

1 To, Dina,’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar.
Dinah, the daughter whom Leah had borne to Jacob, went out to visit the women of the region.
2 Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.
When Shechem the son of Hamor the Hivite, the ruler of the land, saw her, he grabbed her, and raped her, and humiliated her.
3 Zuciyarsa kuwa ta damu da son Dina’yar Yaƙub, ya kuwa ƙaunaci yarinyar, ya yi mata magana a hankali.
Then he became very attached to Dinah, the daughter of Jacob, and he loved the young woman, and spoke kindly to the young woman.
4 Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”
Shechem spoke to his father, Hamor, saying, "Get me this young woman as my wife."
5 Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai’ya’yansa maza sun dawo gida, gama’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo.
Now Jacob heard that he had defiled Dinah, his daughter; and his sons were with his livestock in the field. Jacob remained silent until they came.
6 Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub.
Hamor the father of Shechem went out to Jacob to speak with him.
7 Da’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.
The sons of Jacob came in from the field when they heard it. The men were grieved, and they were very angry, because he had disgraced Israel by sexually assaulting Jacob's daughter; a thing that should not be done.
8 Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura.
Hamor talked with them, saying, "The heart of my son Shechem is set on your daughter. Please give her to him as a wife.
9 Ku yi auratayya da mu; ku aurar mana da’ya’yanku mata, ku kuma ku auro’ya’yanmu mata wa kanku.
Arrange marriages with us. Give your daughters to us, and take our daughters for yourselves.
10 Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.”
You may settle among us, and the land will be open to you. Live and trade in it, and acquire property in it."
11 Sai Shekem ya ce wa mahaifin Dina da kuma’yan’uwanta. “Bari in sami tagomashi a idanunku, zan kuwa ba ku duk abin da kuka tambaya.
Shechem said to her father and to her brothers, "Let me find favor in your sight, and whatever you ask of me I will give.
12 Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.”
Ask me for a very expensive bride price, and I will pay whatever you ask of me, but give me the young woman as a wife."
13 Domin an ɓata’yar’uwansu Dina, sai’ya’yan Yaƙub maza suka amsa a ha’ince yayinda suke wa Shekem da mahaifinsa Hamor magana.
The sons of Jacob replied deceitfully to Shechem and his father Hamor, because he had defiled their sister Dinah.
14 Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, ba za mu iya ba da’yar’uwarmu ga mutumin da ba shi da kaciya ba. Wannan zai zama abin kunya ne a gare mu.
And they said to them, "We can't do this thing, to give our sister to one who is uncircumcised; for that would be a disgrace to us.
15 Za mu yarda da wannan kaɗai ta wannan sharaɗi, cewa za ku zama kamar mu ta wurin yin wa dukan’ya’yanku maza kaciya.
Only on this condition will we agree with you; that you become like us by circumcising all your males;
16 Sa’an nan za mu ba da’ya’yanmu mata aure gare ku, mu kuma mu aure’ya’yanku mata wa kanmu. Za mu zauna a cikinku mu kuma zama mutane ɗaya da ku.
then will we give our daughters to you, and we will take your daughters to ourselves, and we will live among you and become one people.
17 Amma in ba za ku yarda a yi muku kaciya ba, za mu ɗauki’yar’uwanmu mu tafi.”
But if you will not listen to us and be circumcised, then we will take our daughter and go away."
18 Sharuɗansu sun gamshi Hamor da ɗansa, Shekem.
Their words pleased Hamor and Shechem, Hamor's son.
19 Saurayin wanda aka fi girmamawa a cikin dukan gidan mahaifinsa, bai ɓata lokaci a yin abin da suka ce ba, domin ya ji daɗin’yar Yaƙub.
The young man did not delay to do this thing, because he was delighted with Jacob's daughter. Now he was the most important of anyone in his father's house.
20 Saboda haka Hamor da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu don su yi magana da mutanen garinsu.
Hamor and his son Shechem came to the gate of their city, and spoke to the men of their city, saying,
21 Suka ce, “Waɗannan mutane ba su da damuwa, bari su zauna a cikin ƙasarmu, su kuma yi sana’a a ciki; ƙasar tana da isashen fili dominsu. Za mu iya auro’ya’yansu mata, su kuma su auri namu.
"These men are at peace with us. Therefore let them live in the land and travel in it. For look, the land is large enough for them. Let us take their daughters as wives for ourselves, and let us give them our daughters.
22 Amma mutanen za su yarda su zauna tare da mu kamar mutane ɗaya kawai bisa wannan sharaɗi, cewa a yi wa mazanmu kaciya, kamar yadda su kansu suke.
Only on this condition will the men agree to live with us as one people: that every male among us be circumcised, as they are circumcised.
23 Ashe, shanunsu, dukiyarsu da dukan sauran dabbobinsu, ba za su zama namu ba? Saboda haka mu yarda, za su kuwa zauna a cikinmu.”
Won't their livestock and their possessions and all their animals be ours? Only let us agree with them, so they will settle among us."
24 Dukan mazan da suka fito ƙofar birnin suka yarda da Hamor da kuma ɗansa Shekem, aka kuwa yi wa kowane namiji a birnin kaciya.
All who went out of the gate of his city agreed with Hamor and his son Shechem; and every male was circumcised, all who went out of the gate of his city.
25 Bayan kwana uku, yayinda dukansu suna cikin zafi mikin kaciya, sai biyu daga cikin’ya’yan Yaƙub maza, Simeyon da Lawi,’yan’uwan Dina, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka kashe kowane namiji.
It happened on the third day, when they were still in pain, that two of Jacob's sons, Simeon and Levi, Dinah's brothers, each took his sword and came into the unsuspecting city and killed all the males.
26 Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dina daga gidan Shekem suka tafi.
They killed Hamor and his son Shechem with their swords and took Dinah out of Shechem's house and left.
27 Sa’an nan’ya’yan Yaƙub maza suka bi kan gawawwakin, suka washe arzikin birni saboda an ɓata’yar’uwarsu.
Jacob's sons entered over the dead and plundered the city, because they had defiled their sister.
28 Suka kwashe garkunansu na shanu da jakuna, da kuma kome na mutanen a birnin da kuma cikin gonaki.
They took their flocks, their herds, their donkeys, and whatever was in the city and was in the field,
29 Suka kwashe dukan dukiyarsu da dukan matansu da’ya’yansu, suka kwashe kome da yake cikin gidaje.
and all their wealth. They took captive all their little ones and their wives, and took as plunder everything that was in the houses.
30 Sai Yaƙub ya ce wa Simeyon da Lawi, “Kun jawo mini wahala ta wurin sa in zama abin ƙi ga Kan’aniyawa da Ferizziyawa, mazaunan wannan ƙasa. Mu kima ne, in kuwa suka haɗa kai gāba da ni, suka fāɗa mini, za su hallaka ni da gidana.”
Jacob said to Simeon and Levi, "You have brought trouble on me, to make me odious to the inhabitants of the land, among the Canaanites and the Perizzites. I am few in number. They will gather themselves together against me and attack me, and I and my household will be destroyed."
31 Amma’ya’yansa suka amsa, “To, ya dace ke nan da ya yi da’yar’uwarmu kamar karuwa?”
But they said, "Should he treat our sister like a prostitute?"

< Farawa 34 >