< Farawa 33 >

1 Yaƙub ya ɗaga ido ke nan, sai ga Isuwa yana zuwa tare da mutanensa ɗari huɗu; saboda haka sai ya rarraba’ya’yan wa Liyatu, Rahila da kuma matan nan biyu masu hidima.
雅各举目观看,见以扫来了,后头跟着四百人,他就把孩子们分开交给利亚、拉结,和两个使女,
2 Ya sa matan nan biyu masu hidima da’ya’yansu a gaba, Liyatu da’ya’yanta biye, sa’an nan Rahila da Yusuf a baya.
并且叫两个使女和她们的孩子在前头,利亚和她的孩子在后头,拉结和约瑟在尽后头。
3 Shi kansa ya sha gabansu, ya rusuna har ƙasa sau bakwai, kafin ya kai kusa da inda ɗan’uwansa Isuwa yake.
他自己在他们前头过去,一连七次俯伏在地才就近他哥哥。
4 Amma Isuwa ya ruga a guje ya sadu da Yaƙub ya rungume shi; ya faɗa a wuyansa ya sumbace shi. Suka kuma yi kuka.
以扫跑来迎接他,将他抱住,又搂着他的颈项,与他亲嘴,两个人就哭了。
5 Sa’an nan Isuwa ya ɗaga ido ya ga mata da’ya’ya. Ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan tare da kai?” Yaƙub ya amsa, “Su ne’ya’yan da Allah cikin alheri ya ba bawanka.”
以扫举目看见妇人孩子,就说:“这些和你同行的是谁呢?”雅各说:“这些孩子是 神施恩给你的仆人的。”
6 Sai matan nan biyu masu hidima da’ya’yansu suka matso kusa suka durƙusa.
于是两个使女和她们的孩子前来下拜;
7 Biye da su, Liyatu da’ya’yanta suka zo suka rusuna. A ƙarshe duka, sai Yusuf da Rahila suka zo, su ma suka rusuna.
利亚和她的孩子也前来下拜;随后约瑟和拉结也前来下拜。
8 Isuwa ya yi tambaya, “Me kake nufi da dukan abubuwan nan da na sadu da su ana korarsu?” Sai Yaƙub ya ce, “Don in sami tagomashi a idanunka ne, ranka yă daɗe.”
以扫说:“我所遇见的这些群畜是什么意思呢?”雅各说:“是要在我主面前蒙恩的。”
9 Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.”
以扫说:“兄弟啊,我的已经够了,你的仍归你吧!”
10 Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki.
雅各说:“不然,我若在你眼前蒙恩,就求你从我手里收下这礼物;因为我见了你的面,如同见了 神的面,并且你容纳了我。
11 Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.
求你收下我带来给你的礼物;因为 神恩待我,使我充足。”雅各再三地求他,他才收下了。
12 Sa’an nan Isuwa ya ce, “Bari mu tafi, zan yi maka rakiya.”
以扫说:“我们可以起身前往,我在你前头走。”
13 Amma Yaƙub ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ka san cewa’ya’yan ƙanana ne, dole in lura da tumaki da shanun da suke shayar da jariransu. In aka kore su da gaggawa a rana guda kaɗai, dukan dabbobin za su mutu.
雅各对他说:“我主知道孩子们年幼娇嫩,牛羊也正在乳养的时候,若是催赶一天,群畜都必死了。
14 Saboda haka bari ranka yă daɗe yă sha gaban bawansa, ni kuma in tafi a hankali bisa ga saurin abin da ake kora a gabana da kuma saurin’ya’yan, sai na iso wurinka ranka yă daɗe, a Seyir.”
求我主在仆人前头走,我要量着在我面前群畜和孩子的力量慢慢地前行,直走到西珥我主那里。”
15 Sai Isuwa ya ce, “To, bari in bar waɗansu mutanena tare da kai.” Yaƙub ya ce, “Amma me ya sa za ka yi haka? Bari dai in sami tagomashi a idanunka ranka yă daɗe.”
以扫说:“容我把跟随我的人留几个在你这里。”雅各说:“何必呢?只要在我主眼前蒙恩就是了。”
16 Saboda haka a wannan rana Isuwa ya kama hanyar komawa zuwa Seyir.
于是,以扫当日起行,回往西珥去了。
17 Yaƙub kuwa, ya tafi Sukkot, inda ya gina wuri domin kansa, ya kuma yi bukkoki domin dabbobinsa. Shi ya sa aka kira wurin Sukkot.
雅各就往疏割去,在那里为自己盖造房屋,又为牲畜搭棚;因此那地方名叫疏割。
18 Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.
雅各从巴旦·亚兰回来的时候,平平安安地到了迦南地的示剑城,在城东支搭帐棚,
19 Ya sayi fili daga’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa ɗari.
就用一百块银子向示剑的父亲、哈抹的子孙买了支帐棚的那块地,
20 A can ya kafa bagade ya kuma kira shi El Elohe Isra’ila.
在那里筑了一座坛,起名叫伊利·伊罗伊·以色列。

< Farawa 33 >