< Farawa 10 >

1 Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet,’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi’ya’ya maza bayan ambaliyar.
ואלה תולדת בני נח שם חם ויפת ויולדו להם בנים אחר המבול
2 ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai da Yaban, Tubal, Meshek, da kuma Tiras.
בני יפת--גמר ומגוג ומדי ויון ותבל ומשך ותירס
3 ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat, da Togarma.
ובני גמר--אשכנז וריפת ותגרמה
4 ’Ya’yan maza Yaban su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.
ובני יון אלישה ותרשיש כתים ודדנים
5 (Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
מאלה נפרדו איי הגוים בארצתם איש ללשנו--למשפחתם בגויהם
6 ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar, Fut, da Kan’ana.
ובני חם--כוש ומצרים ופוט וכנען
7 ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.’Ya’yan Ra’ama maza kuwa su ne, Sheba da Dedan.
ובני כוש--סבא וחוילה וסבתה ורעמה וסבתכא ובני רעמה שבא ודדן
8 Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
וכוש ילד את נמרד הוא החל להיות גבר בארץ
9 Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
הוא היה גבר ציד לפני יהוה על כן יאמר כנמרד גבור ציד לפני יהוה
10 Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
ותהי ראשית ממלכתו בבל וארך ואכד וכלנה בארץ שנער
11 Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala
מן הארץ ההוא יצא אשור ויבן את נינוה ואת רחבת עיר ואת כלח
12 da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
ואת רסן בין נינוה ובין כלח--הוא העיר הגדלה
13 Mizrayim shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Naftuhiyawa,
ומצרים ילד את לודים ואת ענמים ואת להבים--ואת נפתחים
14 Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
ואת פתרסים ואת כסלחים אשר יצאו משם פלשתים--ואת כפתרים
15 Kan’ana shi ne mahaifin, Sidon ɗan farinsa, da na Hittiyawa,
וכנען ילד את צידן בכרו--ואת חת
16 Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
ואת היבוסי ואת האמרי ואת הגרגשי
17 Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
ואת החוי ואת הערקי ואת הסיני
18 Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa. Daga baya zuriyar Kan’aniyawa suka yaɗu
ואת הארודי ואת הצמרי ואת החמתי ואחר נפצו משפחות הכנעני
19 har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
ויהי גבול הכנעני מצידן--באכה גררה עד עזה באכה סדמה ועמרה ואדמה וצבים--עד לשע
20 Waɗannan su ne’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
אלה בני חם למשפחתם ללשנתם בארצתם בגויהם
21 Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet,’ya’ya maza. Shem shi ne kakan’ya’yan Eber duka.
ולשם ילד גם הוא אבי כל בני עבר--אחי יפת הגדול
22 ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.
בני שם עילם ואשור וארפכשד ולוד וארם
23 ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Mash.
ובני ארם--עוץ וחול וגתר ומש
24 Arfakshad ne mahaifin Shela. Shela kuma shi ne mahaifin Eber.
וארפכשד ילד את שלח ושלח ילד את עבר
25 Aka haifa wa Eber’ya’ya maza biyu. Aka ba wa ɗaya suna Feleg, gama a zamaninsa ne aka raba duniya; aka kuma sa wa ɗan’uwansa suna Yoktan.
ולעבר ילד שני בנים שם האחד פלג כי בימיו נפלגה הארץ ושם אחיו יקטן
26 Yoktan shi ne mahaifin, Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera,
ויקטן ילד את אלמודד ואת שלף ואת חצרמות ואת ירח
27 Hadoram, Uzal, Dikla,
ואת הדורם ואת אוזל ואת דקלה
28 Obal, Abimayel, Sheba,
ואת עובל ואת אבימאל ואת שבא
29 Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan’ya’yan Yoktan maza ne.
ואת אופר ואת חוילה ואת יובב כל אלה בני יקטן
30 Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
ויהי מושבם ממשא באכה ספרה הר הקדם
31 Waɗannan su ne’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
אלה בני שם למשפחתם ללשנתם בארצתם לגויהם
32 Waɗannan su ne zuriyar’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.
אלה משפחת בני נח לתולדתם בגויהם ומאלה נפרדו הגוים בארץ--אחר המבול

< Farawa 10 >