< Ezekiyel 30 >

1 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2 “Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Yi kuka kana cewa, “Kaito saboda wannan rana!” 3 Gama ranar ta yi kusa, ranar Ubangiji ta gabato, ranar gizagizai, lokacin hallaka wa al’ummai. 4 Takobi zai zo a kan Masar, azaba za tă zo a kan Kush. Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar, za a kwashe dukiyarta a tafi a rushe harsashinta. 5 Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar. 6 “‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare. Daga Migdol zuwa Aswan za su mutu ta wurin takobi a cikinta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 7 Za su zama kango a cikin ƙasashen da suke kango, biranensu kuwa za su zama kufai a cikin biranen da suka lalace. 8 Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar aka kuma ragargaza masu taimakonta. 9 “‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo. 10 “‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon. 11 Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai, za a kawo don su hallaka ƙasar. Za su zāre takuba a kan Masar su kuma cika ƙasar da kisassu. 12 Zan kafe rafuffukan Nilu in sayar da ƙasar ga mugayen mutane; ta hannun baƙi zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta. Ni Ubangiji na faɗa. 13 “‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “‘Zan hallaka gumaka in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis. Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba, zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar. 14 Zan lalace Masar ta Bisa in ƙuna wuta wa Zowan in zartar da hukunci a kan Tebes. 15 Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum, kagarar Masar, in kuma datse mutanen Tebes. 16 Zan ƙuna wuta wa Masar; Felusiyum za tă sha azaba mai zafi. Za a tayar wa Tebes da hankali; Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai. 17 Samarin Heliyofolis da Bubastis za su mutu ta wurin takobi, biranen kansu za su tafi bauta. 18 Duhu ne zai zama rana a Tafanes sa’ad da na karye ikon Masar; a can ƙarfin da take fariya zai ƙare. Za a rufe ta da gizagizai ƙauyukanta kuma za su tafi bauta. 19 Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar, za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’” 20 A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 21 “Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi. 22 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa. 23 Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. 24 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa. 25 Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar. 26 Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”

< Ezekiyel 30 >