< Ezekiyel 20 >

1 A shekara ta bakwai, a wata na biyar a rana ta goma, waɗansu dattawan Isra’ila suka zo don su nemi nufin Ubangiji, suka kuwa zauna a ƙasa a gabana.
It happened in the seventh year, in the fifth month, the tenth day of the month, that certain of the elders of Israel came to inquire of Jehovah, and sat before me.
2 Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
The word of Jehovah came to me, saying,
3 “Ɗan mutum, ka yi magana da dattawan Isra’ila ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kun zo ne ku nemi shawarata? Muddin ina raye, ba zan bari ku nemi shawarata ba, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’
"Son of man, speak to the elders of Israel, and tell them, 'Thus says Jehovah: "Is it to inquire of me that you have come? As I live, says Jehovah, I will not be inquired of by you."'
4 “Za ka hukunta su? Za ka hukunta su, ɗan mutum? To, sai ka kalubalance su da ayyukan banƙyamar kakanninsu
Will you judge them, son of man, will you judge them? Cause them to know the abominations of their fathers;
5 ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da na zaɓi Isra’ila, na ɗaga hannuna, na rantse wa zuriyar gidan Yaƙub na kuma bayyana kaina gare su a Masar da hannun da na ɗaga na ce musu, “Ni ne Ubangiji Allahnku.”
and tell them, 'Thus says Jehovah: "In the day when I chose Israel, and swore to the offspring of the house of Jacob, and made myself known to them in the land of Egypt, when I swore to them, saying, 'I am Jehovah your God';
6 A ranar na yi musu rantsuwa cewa zan fitar da su daga Masar zuwa ƙasar da na samo musu, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe.
in that day I swore to them, to bring them forth out of the land of Egypt into a land that I had searched out for them, flowing with milk and honey, which is the glory of all lands.
7 Na kuma ce musu, “Kowannenku ya zubar da mugayen siffofin da kuka kafa idanunku a kai, kuma kada ku ƙazantar da kanku da gumakan Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
I said to them, 'Cast away every man the abominations of his eyes, and do not defile yourselves with the idols of Egypt; I am Jehovah your God.'
8 “‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar.
But they rebelled against me, and would not listen to me; they each didn't throw away the abominations of their eyes, neither did they forsake the idols of Egypt. Then I said I would pour out my wrath on them, to accomplish my anger against them in the midst of the land of Egypt.
9 Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da suka zauna a ciki da kuma a idanun al’ummai da na bayyana kaina ga Isra’ilawa ta wurin fitar da su daga Masar.
But I worked for my name's sake, that it should not be profaned in the sight of the nations, among which they were, in whose sight I made myself known to them, in bringing them forth out of the land of Egypt.
10 Saboda haka na fisshe su daga Masar na kawo su cikin hamada.
"'"So I caused them to go forth out of the land of Egypt, and brought them into the wilderness.
11 Na ba su ƙa’idodina na kuma sanar musu da dokokina, gama mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu.
I gave them my statutes, and showed them my ordinances, which if a man does, he shall live in them.
12 Na kuma ba su Asabbataina kamar alama tsakaninmu, domin su san cewa Ni Ubangiji ne yake tsarkake su.
Moreover also I gave them my Sabbaths, to be a sign between me and them, that they might know that I am Jehovah who sanctifies them.
13 “‘Duk da haka mutanen Isra’ila suka yi mini tawaye a cikin hamada. Ba su bi ƙa’idodina ba amma suka ki dokokina, ko da yake mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu, suka ɓata Asabbataina ƙwarai. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma hallaka su a hamada.
But the house of Israel rebelled against me in the wilderness: they didn't walk in my statutes, and they rejected my ordinances, which if a man keep, he shall live in them; and my Sabbaths they greatly profaned. Then I said I would pour out my wrath on them in the wilderness, to consume them.
14 Amma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su.
But I worked for my name's sake, that it should not be profaned in the sight of the nations, in whose sight I brought them out.
15 Na kuma ɗaga hannu na rantse musu a hamada cewa ba zan kawo su ƙasar da na ba su ba, ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasa mafi kyau cikin dukan ƙasashe,
"'"Moreover also I swore to them in the wilderness, that I would not bring them into the land which I had given to them, flowing with milk and honey, which is the most beautiful of all lands;
16 domin sun ƙi dokokina ba su kuwa bi ƙa’idodina ba suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Gama zukatansu sun fi so su bauta wa gumakansu.
because they rejected my ordinances, and didn't walk in my statutes, and profaned my Sabbaths: for their heart went after their idols.
17 Duk da haka na dube su ta tausayi ba zan hallaka su ko in kawo ƙarshensu a hamada ba.
Nevertheless my eye spared them, and I didn't destroy them, neither did I make a full end of them in the wilderness.
18 Na faɗa wa’ya’yansu a hamada, “Kada ku bi farillai kakanninku ko ku kiyaye dokokinsu ko ku ƙazantar da kanku da gumakansu.
"'"I said to their children in the wilderness, 'Do not walk in the statutes of your fathers, neither observe their ordinances, nor defile yourselves with their idols.
19 Ni ne Ubangiji Allahnku; ku bi ƙa’idodina ku kuma kula ku kiyaye dokokina.
I am Jehovah your God: walk in my statutes, and keep my ordinances, and do them;
20 Ku kiyaye Asabbataina da tsarki, don su zama alama tsakaninmu. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Allahnku.”
and make my Sabbaths holy; and they shall be a sign between me and you, that you may know that I am Jehovah your God.'
21 “‘Amma’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada.
But the children rebelled against me; they didn't walk in my statutes, neither kept my ordinances to do them, which if a man do, he shall live in them; and they profaned my Sabbaths. Then I said I would pour out my wrath on them, to accomplish my anger against them in the wilderness.
22 Amma na janye hannuna, kuma saboda sunana na yi abin da zai kiyaye shi daga ƙazantuwa a idanun al’umman da a idonsu na fisshe su.
Nevertheless I withdrew my hand, and worked for my name's sake, that it should not be profaned in the sight of the nations, in whose sight I brought them forth.
23 Na kuma ɗaga hannu na rantse musu cewa zan watsar da su cikin al’ummai in kuma warwatsa su cikin ƙasashe,
Moreover I swore to them in the wilderness, that I would scatter them among the nations, and disperse them through the countries;
24 domin ba su kiyaye dokokina ba amma suka ƙi ƙa’idodina suka kuma ƙazantar da Asabbataina, idanunsu suka yi sha’awar gumakan kakanninsu.
because they had not executed my ordinances, but had rejected my statutes, and had profaned my Sabbaths, and their eyes were after their fathers' idols.
25 Na kuma ba da su ga farillan da ba su da kyau da dokokin da ba za su rayu ta wurinsu ba;
Moreover also I gave them statutes that were not good, and ordinances in which they should not live;
26 na bari suka ƙazantu ta wurin kyautai, hadayar kowane ɗan fari don in cika su da abin tsoro domin su san cewa ni ne Ubangiji.’
and I polluted them in their own gifts, in that they caused to pass through the fire all that opens the womb, that I might make them desolate, to the end that they might know that I am Jehovah."'
27 “Saboda haka, ɗan mutum, ka yi magana da mutanen Isra’ila ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a wannan kuma kakanninku suka saɓe ni ta wurin yashe ni.
"Therefore, son of man, speak to the house of Israel, and tell them, 'Thus says Jehovah: "In this moreover have your fathers blasphemed me, in that they have committed a trespass against me.
28 Sa’ad da na kawo su cikin ƙasar da na rantse zan ba su suka kuma ga tudu mai tsawo ko itace mai ganye, a can suka miƙa hadayunsu, suka yi sadakokin da suka tsokane ni na yi fushi, suka miƙa turaren ƙanshinsu suka kuma zuba sadakokinsu na sha.
For when I had brought them into the land, which I swore to give to them, then they saw every high hill, and every thick tree, and they offered there their sacrifices, and there they presented the provocation of their offering; there also they made their pleasant aroma, and they poured out there their drink offerings.
29 Sai na ce musu, Wane ɗakin tsafi kuke tafiya?’” (Ana ce da shi Bama har wa yau.)
Then I said to them, 'What does the high place where you go mean?' So its name is called Bamah to this day."'
30 “Domin haka ka faɗa wa gidan Isra’ila, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa za ku ƙazantar da kanku yadda kakanninku suka yi ne ku yi sha’awar mugayen siffofinsu?
"Therefore tell the house of Israel, 'Thus says Jehovah: "Do you pollute yourselves in the way of your fathers? And do you play the prostitute after their abominations?
31 Sa’ad da kuka miƙa kyautai naku, hadayar’ya’yanku maza a wuta, kuna cin gaba da ƙazantar da kanku da duka gumakanku har wa yau. Zan bari ku nemi shawarata, ya gidan Isra’ila? Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba zan bari ku nemi shawarata ba.
And when you offer your gifts, when you make your sons to pass through the fire, do you pollute yourselves with all your idols to this day? And shall I be inquired of by you, house of Israel? As I live, says Jehovah, I will not be inquired of by you;
32 “‘Kukan ce, “Kuna so ku zama kamar sauran al’ummai, kamar sauran mutanen duniya, waɗanda suke bauta wa itace da dutse.” Amma abin da kuke tunani ba zai taɓa faruwa ba.
and that which comes into your mind shall not be at all, in that you say, 'We will be as the nations, as the families of the countries, to serve wood and stone.'
33 Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, zan yi mulki a kanku da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi.
As I live," says Jehovah, "surely with a mighty hand, and with an outstretched arm, and with wrath poured out, will I be king over you:
34 Zan fitar da ku daga al’ummai in tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, da hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi da kuma fushi.
and I will bring you out from the peoples, and will gather you out of the countries in which you are scattered, with a mighty hand, and with an outstretched arm, and with wrath poured out;
35 Zan kawo ku cikin hamadar al’ummai a can kuwa, fuska da fuska, zan hukunta ku.
and I will bring you into the wilderness of the peoples, and there will I enter into judgment with you face to face.
36 Yadda na hukunta kakanninku a hamadar ƙasar Masar, haka zan hukunta ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
Like as I entered into judgment with your fathers in the wilderness of the land of Egypt, so will I enter into judgment with you," says Jehovah.
37 Zan lura da ku yayinda kuke wucewa ƙarƙashin sanda, zan kuma kawo ku cikin daurin alkawari.
"I will cause you to pass under the rod, and I will bring you into the bond of the covenant;
38 Zan fitar da waɗanda suke mini tayarwa da kuma’yan tawaye. Ko da yake zan fitar da su daga ƙasar da suke zama, duk da haka ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.
and I will purge out from among you the rebels, and those who disobey against me; I will bring them forth out of the land where they live, but they shall not enter into the land of Israel: and you shall know that I am Jehovah."
39 “‘Game da ku, ya gidan Isra’ila, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ku tafi ku bauta wa gumakanku, kowannenku! Amma daga baya tabbatacce za ku saurare ni ba kuwa za ku ƙara ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku ba.
"'As for you, house of Israel, thus says the Lord Jehovah: "Go, serve everyone his idols, and hereafter also, if you will not listen to me; but my holy name you shall no more profane with your gifts, and with your idols.
40 Gama a kan dutsena mai tsarki, dutse mai tsayi na Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, a can a ƙasar gidan Isra’ila gaba ɗaya za su bauta mini, a can kuwa zan karɓe su. A can zan bukaci hadayunku da sadake sadakenku mafi kyau, tare da dukan tsarkakan hadayunku.
For in my holy mountain, in the mountain of the height of Israel," says Jehovah, "there shall all the house of Israel, all of them, serve me in the land: there will I accept them, and there will I require your offerings, and the first fruits of your offerings, with all your holy things.
41 Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa’ad da na fitar da ku daga al’ummai na kuma tattara ku daga ƙasashe inda aka warwatsa ku, zan kuma nuna kaina mai tsarki a cikinku a idon al’ummai.
As a pleasant aroma will I accept you, when I bring you out from the peoples, and gather you out of the countries in which you have been scattered; and I will be sanctified in you in the sight of the nations.
42 Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na kawo ku cikin ƙasar Isra’ila, ƙasar da na ɗaga hannu na rantse zan ba wa kakanninku.
You shall know that I am Jehovah, when I shall bring you into the land of Israel, into the country which I swore to give to your fathers.
43 A can za ku tuna da halinku da kuma dukan ayyukanku waɗanda kuka ɓata kanku da su, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwan da kuka aikata.
There you shall remember your ways, and all your doings, in which you have polluted yourselves; and you shall loathe yourselves in your own sight for all your evils that you have committed.
44 Za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na yi muku haka saboda sunana ba bisa ga mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau ba, ya gidan Isra’ila, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’”
You shall know that I am Jehovah, when I have dealt with you for my name's sake, not according to your evil ways, nor according to your corrupt doings, you house of Israel," says Jehovah.'"
45 Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
The word of Jehovah came to me, saying,
46 “Ɗan mutum, ka kafa fuskarka wajen kudu; ka yi wa’azi a kan kudu ka kuma yi annabci a kan kurmin ƙasar kudu.
"Son of man, set your face toward the south, and drop your word toward the south, and prophesy against the forest of the field in the South;
47 Ka faɗa wa kurmin kudanci, ‘Ji maganar Ubangiji. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da sa maka wuta, za tă kuwa cinye dukan itatuwanki sarai, da ɗanye da busasshe. Ba za a kashe wutar da take ci ba, kuma kowace fuska a kudu zuwa arewa za tă ƙone.
and tell the forest of the South, 'Hear the word of Jehovah: Thus says Jehovah, "Look, I will kindle a fire in you, and it shall devour every green tree in you, and every dry tree: the flaming flame shall not be quenched, and all faces from the south to the north shall be burnt thereby.
48 Kowa zai san cewa Ni Ubangiji ne ya ƙuna ta; ba za a kashe ta ba.’”
All flesh shall see that I, Jehovah, have kindled it; it shall not be quenched."'"
49 Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka! Suna zance a kaina cewa, ‘Ba misalai kawai yake yi ba?’”
Then I said, "Ah, Jehovah. They say of me, 'Isn't he a speaker of parables?'"

< Ezekiyel 20 >