< Ezekiyel 2 >

1 Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.” 2 Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana. 3 Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau. 4 Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’ 5 Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu. 6 Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye. 7 Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su’yan tawaye ne. 8 Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.” 9 Sai na duba, na kuma ga hannu ya miƙe zuwa wurina. A cikinsa akwai littafi, 10 wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito.

< Ezekiyel 2 >