< Amos 1 >

1 Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila. 2 Ya ce, “Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.” 3 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Damaskus, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Domin sun ci zalunci Gileyad zalunci mai tsanani, 4 zan sa wuta a gidan Hazayel, da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad. 5 Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus; zan hallaka sarkin da yake cikin Kwarin Awen da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden. Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,” in ji Ubangiji. 6 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Gaza, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun sayar wa Edom, 7 Zan aika da wuta a katangar Gaza ta ƙone duk kagarunta. 8 Zan hallaka sarkin Ashdod da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. Zan hukunta Ekron, har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka. 9 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Taya, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar’yan’uwa ba, 10 zan aika da wuta a Taya, da za tă ƙone kagarunta.” 11 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Edom, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, babu tausayi, domin ya ci gaba da fusata bai yarda yă huce daga fushinsa ba. 12 Zan aika wuta a Teman da za tă ƙone kagarun Bozra.” 13 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar. 14 Zan sa wuta a katangar Rabba da za tă ƙone kagarunta za a yi kururuwa a ranar yaƙi, faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri. 15 Sarkinta zai je bauta, shi da ma’aikatansa,” in ji Ubangiji.

< Amos 1 >