< Ayyukan Manzanni 10 >

1 A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya.
At Caesarea there was a man named Cornelius, a centurion in the regiment known as the “Italian Regiment,”
2 Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa.
A religious man and one who reverenced God, with all his household. He was liberal in his charities to the people, and prayed to God constantly.
3 Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”
One afternoon, about three o’clock, he distinctly saw in a vision an angel from God come to him, and call him by name.
4 Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.
Cornelius fixed his eyes on him and, in great alarm, said, ‘What is it, Lord?’ ‘Your prayers and your charities,’ the angel answered, ‘have been an acceptable offering to God.
5 Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus.
And now, send messengers to Joppa and fetch a man called Simon, who is also known as Peter.
6 Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.”
He is lodging with a tanner named Simon, who has a house near the sea.’
7 Sa’ad da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima.
When the angel, who had spoken to him, had gone, Cornelius called two servants and a religious soldier, who was one of his constant attendants,
8 Ya fada musu duk abin da ya faru sa’an nan ya aike su Yoffa.
and, after telling them the whole story, sent them to Joppa.
9 Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a.
On the next day, while these men were on their way, just as they were nearing the town, Peter went up on the housetop about midday to pray.
10 Yunwa ta kama shi ya kuwa so yă ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa.
He became hungry and wanted something to eat; but while it was being prepared, he fell into a trance,
11 Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu.
and saw that the heavens were open, and that something like a great sail was descending, let down by its four corners towards the earth.
12 Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama.
In it were all kinds of quadrupeds, reptiles, and birds.
13 Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”
Then he was aware of a voice which said – ‘Stand up, Peter, kill something, and eat.’
14 Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”
‘No, Lord, I cannot,’ answered Peter, ‘for I have never eaten anything defiled and unclean.’
15 Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”
Again he was aware of a voice which said – ‘What God has pronounced clean, do not regard as defiled.’
16 Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama.
This happened three times, and then suddenly it was all taken up into the heavens.
17 Tun Bitrus yana cikin tunani game da ma’anar wahayin nan, sai ga mutanen da Korneliyus ya aika sun sami gidan Siman suna kuma tsaye a ƙofar.
While Peter was still perplexed as to the meaning of the vision that he had seen, the men sent by Cornelius, having enquired the way to Simon’s house, came up to the gate,
18 Suka yi sallama, suna tambaya ko Siman wanda aka sani da suna Bitrus yana zama a can.
and called out and asked if the Simon, who was also known as Peter, was lodging there.
19 Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka.
Peter was still pondering over the vision, when the Spirit said to him, ‘There are two men looking for you at this moment.
20 Saboda haka ka tashi ka sauka. Kada ka yi wata-wata, gama ni ne na aiko su.”
Go down at once and do not hesitate to go with them, for I have sent them.’
21 Sai Bitrus ya sauka ya ce wa mutanen, “Ni ne kuke nema. Me ya kawo ku?”
Peter went down to the men and said, ‘I am the person you are looking for. What is your reason for coming?’
22 Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani mala’ika mai tsarki ya faɗa masa, yă sa ka zo gidansa don yă ji abin da za ka faɗa.”
The men replied, ‘Our centurion, Cornelius, a pious man who reverences God and is well spoken of by the whole Jewish nation, has been instructed by a holy angel to send for you to his house, and to listen to what you have to say.’
23 Sai Bitrus ya gayyaci mutanen cikin gida su zama baƙinsa. Kashegari Bitrus ya tafi tare da su, waɗansu’yan’uwa daga Yoffa kuwa suka tafi tare da shi.
So Peter invited them in and entertained them. The next day he lost no time in setting out with them, accompanied by some of the Lord’s followers from Joppa;
24 Kashegari sai ya iso Kaisariya. Korneliyus kuwa yana nan yana jiransu, ya kuma gayyaci’yan’uwansa da abokansa na kusa.
and the day following he entered Caesarea. Cornelius was expecting them, and had invited his relatives and intimate friends to meet them.
25 Da Bitrus ya shiga gidan, Korneliyus ya sadu da shi ya kuma fāɗi a gabansa cikin bangirma.
So, when Peter entered the city, Cornelius met him, and, throwing himself at Peter’s feet, bowed to the ground.
26 Amma Bitrus ya sa shi ya tashi. Ya ce, “Tashi, ni mutum ne kawai.”
Peter, however, lifted him up, saying as he did so, ‘Stand up, I am only human like yourself.’
27 Yana magana da shi, sai Bitrus ya shiga ciki ya kuma tarar da taron mutane da yawa.
Talking with him as he went, Peter entered the house, where he found a large gathering of people, to whom he said,
28 Sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana mutumin Yahuda yin cuɗanya, ko ya ziyarci Ba’al’umme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta.
‘You are doubtless aware that it is forbidden for a Jew to be intimate with a foreigner, or even to enter his house; and yet God has shown me that I ought not to call anyone defiled or unclean.
29 Don haka sa’ad da aka aika in zo, na zo ba wata faɗa. To, ko zan san abin da ya sa ka aika in zo?”
That was why I came, when I was sent for, without raising any objection. And now I ask your reason for sending for me.’
30 Korneliyus ya amsa ya ce, “Kwana huɗu da suka wuce ina a gidana ina addu’a a wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma. Ba zato ba tsammani sai ga wani mutum cikin tufafi masu walƙiya ya tsaya a gabana
‘Just three days ago this very hour,’ Cornelius said, ‘I was in my house, saying the Afternoon Prayers, when a man in dazzling clothing suddenly stood before me.
31 ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta.
“Cornelius,” he said, “your prayer has been heard, and your charities have been accepted, by God.
32 Ka aika zuwa Yoffa don a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman mai aikin fatu, wanda yake zama a bakin teku.’
Therefore send to Joppa, and invite the Simon, who is also known as Peter, to come here. He is lodging in the house of Simon the tanner, near the sea.”
33 Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.”
Accordingly I sent to you at once, and you have been so good as to come. And now we are all here in the presence of God, to listen to all that you have been instructed by the Lord to say.’
34 Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai
Then Peter began. ‘I see, beyond all doubt,’ he said, ‘that God does not show partiality,
35 amma yana karɓan mutane daga kowace al’ummar da take tsoronsa suke kuma aikata abin da yake daidai.
but that in every nation he who reverences him and does what is right is acceptable to him.
36 Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.
God has sent his message to the Israelites and told them, through Jesus Christ, the good news of peace – and Jesus is Lord of all!
37 Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi,
You yourselves know the story which spread through all Judea, how, beginning form Galilee, after the baptism which John proclaimed –
38 yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.
the story, I mean, of Jesus of Nazareth, and how God consecrated him his Christ by enduing him with the Holy Spirit and with power; and how he went about doing good and curing all who were under the power of the devil, because God was with him.
39 “Mu kuwa shaidu ne na dukan abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da kuma a Urushalima. Suka kashe shi ta wurin rataye shi a kan itace,
We are ourselves, too, witnesses to all that he did in Judea and in Jerusalem; yet they put him to death by hanging him on a cross!
40 amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi.
This Jesus God raised on the third day, and enabled him to appear,
41 Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa, ta wurinmu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu.
not indeed to everyone, but to witnesses chosen beforehand by God – to us, who ate and drank with him after his resurrection from the dead.
42 Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu.
Further, God charged us to proclaim to the people, and solemnly affirm, that it is Jesus who has been appointed by God judge of the living and the dead.
43 Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”
To him it is that all the prophets bear witness, when they say that everyone who believes in him receives through his name forgiveness of sins.’
44 Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon.
Before Peter had finished saying these words, the Holy Spirit fell on all who were listening to the message.
45 Masu bin da suke da kaciya waɗanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki cewa an ba da kyautar Ruhu Mai Tsarki har ma a kan Al’ummai.
Those converts from Judaism, who had come with Peter, were amazed that the gift of the Holy Spirit had been bestowed even on the Gentiles;
46 Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah. Sai Bitrus ya ce,
for they heard them speaking in different languages and extolling God. At this Peter asked,
47 “Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.”
‘Can anyone refuse the water for the baptism of these people, now that they have received the Holy Spirit as we did ourselves?’
48 Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Sa’an nan suka roƙi Bitrus yă zauna da su na’yan kwanaki.
And he directed that they should be baptized in the name of Jesus Christ; after which they asked him to stay there a few days longer.

< Ayyukan Manzanni 10 >