< 2 Sama’ila 5 >

1 Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu nama da jininka ne.
Then all the tribes of Israel came to David at Hebron, saying, "Look, we are your bone and your flesh.
2 A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’”
In times past, when Saul was king over us, it was you who led out and brought in Israel. The LORD said to you, 'You shall be shepherd of my people Israel, and you shall be ruler over Israel.'"
3 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, sarki ya yi yarjejjeniya da su a gaban Ubangiji, suka kuwa naɗa Dawuda sarki bisa Isra’ila.
So all the elders of Israel came to the king to Hebron; and king David made a covenant with them in Hebron before the LORD; and they anointed David king over Israel.
4 Dawuda yana da shekara talatin ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara arba’in.
David was thirty years old when he began to reign, and he reigned forty years.
5 A Hebron ya yi mulki a bisa Yahuda shekara bakwai da wata shida, a Urushalima kuma ya yi mulki a bisa Isra’ila da Yahuda shekara talatin da uku.
In Hebron he reigned over Judah seven years and six months; and in Jerusalem he reigned thirty-three years over all Israel and Judah.
6 Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.”
The king and his men went to Jerusalem against the Jebusites, the inhabitants of the land, who spoke to David, saying, "You will not come in here, but the blind and the lame will repel you"; thinking, "David can't come in here."
7 Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda.
Nevertheless David took the stronghold of Zion, that is, the City of David.
8 A ranar, Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kame Yebusiyawa, dole yă yi amfani da wuriyar ruwa don yă kai ga waɗannan ‘guragu da makafi’ waɗanda suke abokan gāban Dawuda.” Shi ya sa suka ce, “‘Makafi da guragu’ ba za su shiga fadan sarki ba.”
David said on that day, "Whoever strikes the Jebusites, let him get up to the watercourse, and strike the lame and the blind, those who hate the soul of David." Therefore they say, "The blind and the lame can't come into the palace."
9 Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki.
David lived in the stronghold, and called it the City of David. And he built a city all around from the Millo and inward.
10 Ya yi ta ƙara ƙarfi, gama Ubangiji Allah Maɗaukaki yana tare da shi.
David grew greater and greater; for the LORD of hosts was with him.
11 To, Hiram sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda tare da gumaguman itacen al’ul, da kafintoci, da kuma maginan duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda fada.
Hiram king of Tyre sent messengers to David, and cedar trees, and craftsmen of wood, and craftsmen of a wall; and they built David a palace.
12 Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya naɗa shi sarki bisa Isra’ila, ya kuma ɗaukaka masarautarsa saboda mutanensa Isra’ila.
And David knew that the LORD had established him king over Israel, and that he had exalted his kingdom for his people Israel's sake.
13 Bayan ya bar Hebron, Dawuda ya ƙara ɗauko wa kansa waɗansu ƙwarƙwarai da mata a Urushalima. Aka haifa masa’ya’ya maza da mata.
David took more secondary wives and wives out of Jerusalem, after he had come from Hebron; and there were born to David more sons and daughters.
14 Waɗannan su ne sunayen’ya’yan da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,
These are the names of those who were born to him in Jerusalem: Shammua, and Shobab, and Nathan, and Solomon,
15 Ibhar, Elishuwa, Nefeg, Yafiya,
and Ibhar, and Elishua, and Eliphelet, and Nogah, and Nepheg, and Japhia,
16 Elishama, Eliyada da Elifelet.
and Elishama, and Baaliada, and Eliphelet.
17 Da Filistiyawa suka ji labari an shafe Dawuda sarki a bisa Isra’ila, sai suka haura da ƙarfi sosai don su nema shi, amma Dawuda ya ji labarin sai ya gangara zuwa mafaka.
When the Philistines heard that David had been anointed king over Israel, all the Philistines went up to seek David; and David heard of it, and went down to the stronghold.
18 To, fa, Filistiyawa suka zo suka baje ko’ina a cikin Kwarin Refayim;
Now the Philistines came and spread out in the Valley of Rephaim.
19 saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.”
David inquired of the LORD, saying, "Shall I go up against the Philistines? Will you deliver them into my hand?" The LORD said to David, "Go up; for I will certainly deliver the Philistines into your hand."
20 Saboda haka Dawuda ya tafi Ba’al-Ferazim, a can ya ci su da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa yakan fasu, haka Ubangiji ya kakkarya abokan gābana a gabana.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.
David came to Baal Perazim, and David struck them there; and he said, "The LORD has broken through my enemies before me, like a breakthrough of waters." Therefore he called the name of that place Baal Perazim.
21 Filistiyawa suka bar gumakansu a can, Dawuda da mutanensa kuwa suka kwashe su.
And they abandoned their idols there; and David and his men took them away.
22 Har yanzu Filistiyawa suka sāke haurawa suka bazu a Kwarin Refayim;
The Philistines came up yet again, and spread themselves in the Valley of Rephaim.
23 saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya kuwa ce, “Kada ka haura kai tsaye, amma ka kewaya ta bayansu ka fāɗa musu a gaban itatuwan balsam.
And David inquired of the LORD, and the LORD said to him, "You shall not go up. Circle around behind them, and attack them opposite the poplar trees.
24 Da zarar ka ji tafiya kamar na takawar sojoji tana a bisan itatuwan balsam, sai ka yi maza, gama wannan alama ce cewa Ubangiji ya sha gabanka don yă karkashe sojojin Filistiyawa.”
And it shall be, when you hear the sound of marching in the tops of the poplar trees, that then you are to act decisively; for then the LORD has gone out before you to strike the army of the Philistines."
25 Saboda haka Dawuda ya aikata yadda Ubangiji ya umarce shi, ya kuma karkashe Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.
David did so, as the LORD commanded him, and struck the Philistines from Geba as far as the approach to Gezer.

< 2 Sama’ila 5 >