< 2 Sama’ila 23 >

1 Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe. “Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai, abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama. Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki, wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila.
以下是大卫末了的话。耶西的儿子大卫得居高位,是雅各 神所膏的,作以色列的美歌者,说:
2 “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina; maganarsa tana a harshena.
耶和华的灵借着我说: 他的话在我口中。
3 Allah na Isra’ila ya yi magana, Dutsen Isra’ila ya ce mini, ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci, sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,
以色列的 神、 以色列的磐石晓谕我说: 那以公义治理人民的, 敬畏 神执掌权柄,
4 yana kama da hasken safiya a safiya marar girgije, kamar haske bayan ruwan sama da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’
他必像日出的晨光, 如无云的清晨, 雨后的晴光, 使地发生嫩草。
5 “Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba? Ashe, Allah bai yi madawwamiyar yarjejjeniya da ni shiryayye da ɗaurarre a kowane sashi ba? Ba zai kawo ga cikar cetona yă kuma biya duk bukatuna ba?
我家在 神面前并非如此; 神却与我立永远的约。 这约凡事坚稳, 关乎我的一切救恩和我一切所想望的, 他岂不为我成就吗?
6 Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan da ba a tattara da hannu.
但匪类都必像荆棘被丢弃; 人不敢用手拿它;
7 Duk wanda ya taɓa ƙaya yakan yi amfani da wani ƙarfe ne ko sandar māshi; akan ƙone su inda suke a zube.”
拿它的人必带铁器和枪杆, 终久它必被火焚烧。
8 Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.
大卫勇士的名字记在下面:他革扪人约设·巴设,又称伊斯尼人亚底挪,他是军长的统领,一时击杀了八百人。
9 Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,
其次是亚合人朵多的儿子以利亚撒。从前非利士人聚集要打仗,以色列人迎着上去,有跟随大卫的三个勇士向非利士人骂阵,其中有以利亚撒。
10 amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.
他起来击杀非利士人,直到手臂疲乏,手黏住刀把。那日耶和华使 以色列人大获全胜;众民在以利亚撒后头专夺财物。
11 Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa.
其次是哈拉人亚基的儿子沙玛。一日,非利士人聚集成群,在一块长满红豆的田里,众民就在非利士人面前逃跑。
12 Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.
沙玛却站在那田间击杀非利士人,救护了那田。耶和华使 以色列人大获全胜。
13 A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.
收割的时候,有三十个勇士中的三个人下到亚杜兰洞见大卫。非利士的军兵在利乏音谷安营。
14 Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.
那时大卫在山寨,非利士人的防营在伯利恒。
15 Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”
大卫渴想,说:“甚愿有人将伯利恒城门旁、井里的水打来给我喝。”
16 Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.
这三个勇士就闯过非利士人的营盘,从伯利恒城门旁的井里打水,拿来奉给大卫。他却不肯喝,将水奠在耶和华面前,
17 Sai ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.
说:“耶和华啊,这三个人冒死去打水;这水好像他们的血一般,我断不敢喝。”如此,大卫不肯喝。这是三个勇士所做的事。
18 Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.
洗鲁雅的儿子、约押的兄弟亚比筛是这三个勇士的首领;他举枪杀了三百人,就在三个勇士里得了名。
19 Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
他在这三个勇士里是最尊贵的,所以作他们的首领,只是不及前三个勇士。
20 Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.
有甲薛勇士耶何耶大的儿子比拿雅行过大能的事;他杀了摩押人亚利伊勒的两个儿子,又在下雪的时候下坑里去,杀了一个狮子,
21 Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.
又杀了一个强壮的埃及人;埃及人手里拿着枪,比拿雅只拿着棍子下去,从埃及人手里夺过枪来,用那枪将他杀死。
22 Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.
这是耶何耶大的儿子比拿雅所行的事,就在三个勇士里得了名。
23 Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
他比那三十个勇士都尊贵,只是不及前三个勇士。大卫立他作护卫长。
24 Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,
三十个勇士里有约押的兄弟亚撒黑,伯利恒人朵多的儿子伊勒哈难,
25 Shamma, mutumin Harod, Elika, mutumin Harod,
哈律人沙玛,哈律人以利加,
26 Helez, mutumin Falti, Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa,
帕勒提人希利斯,提哥亚人益吉的儿子以拉,
27 Abiyezer, mutumin Anatot, da Mebunnai, mutumin Husha,
亚拿突人亚比以谢,户沙人米本乃,
28 Zalmon, mutumin Aho, da Maharai, mutumin Netofa,
亚合人撒们,尼陀法人玛哈莱,
29 Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa, Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin,
尼陀法人巴拿的儿子希立,便雅悯族、基比亚人利拜的儿子以太,
30 Benahiya, mutumin Firaton, da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash,
比拉顿人比拿雅,迦实溪人希太,
31 Abi-Albon, mutumin Arba, da Azmawet, mutumin Bahurim,
伯·亚拉巴人亚比亚本,巴鲁米人押斯玛弗,
32 Eliyaba, mutumin Sha’albo,’Ya’yan Yashen, Yonatan,
沙本人以利雅哈巴,雅善儿子中的约拿单,
33 ɗan Shamma mutumin Harar, da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod.
哈拉人沙玛,哈拉人沙拉的儿子亚希暗,
34 Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka, Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo,
玛迦人亚哈拜的儿子以利法列,基罗人亚希多弗的儿子以连,
35 Hezro, mutumin Karmel, Fa’arai, mutumin Arbi,
迦密人希斯莱,亚巴人帕莱,
36 Igal, ɗan Natan mutumin Zoba, ɗan Hagiri,
琐巴人拿单的儿子以甲,迦得人巴尼,
37 Zelek, mutumin Ammon Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,
亚扪人洗勒,比录人拿哈莱(是给洗鲁雅的儿子约押拿兵器的),
38 Ira, mutumin Itra. Gareb, mutumin Itra,
以帖人以拉,以帖人迦立,
39 da kuma Uriya, mutumin Hitti. Su talatin da bakwai ne duka.
赫人乌利亚,共有三十七人。

< 2 Sama’ila 23 >