< 2 Sarakuna 11 >

1 Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta.
Now when Athaliah the mother of Ahaziah saw that her son was dead, she arose and destroyed all the seed royal.
2 Amma Yehosheba,’yar Sarki Yoram,’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.
But Jehosheba, the daughter of king Joram, sister of Ahaziah, took Joash the son of Ahaziah, and stole him away from among the king's sons that were slain, even him and his nurse, and put them in the bed-chamber; and they hid him from Athaliah, so that he was not slain.
3 Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
And he was with her hid in the house of the LORD six years; and Athaliah reigned over the land.
4 A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.
And in the seventh year Jehoiada sent and fetched the captains over hundreds, of the Carites and of the guard, and brought them to him into the house of the LORD; and he made a covenant with them, and took an oath of them in the house of the LORD, and showed them the king's son.
5 Ya umarce su cewa, “Ga abin da za ku yi sa’ad da kuka zo aiki a Asabbaci, ku raba kanku kashi uku. Kashi ɗaya za su yi gadin gidan sarki,
And he commanded them, saying: 'This is the thing that ye shall do: a third part of you, that come in on the sabbath, and that keep the watch of the king's house —
6 kashi ɗaya za su yi gadin Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma za su yi gadin ƙofar da take bayan’yan gadin fada. Dukan waɗannan ƙungiyoyi uku za su yi gadin fadan,
now another third part was at the gate Sur, and another third part at the gate behind the guard — shall keep the watch of the house, and be a barrier.
7 ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki.
And the other two parts of you, even all that go forth on the sabbath, shall keep the watch of the house of the LORD about the king.
8 Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.”
And ye shall compass the king round about, every man with his weapons in his hand; and he that cometh within the ranks, let him be slain; and be ye with the king when he goeth out, and when he cometh in.'
9 Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist.
And the captains over hundreds did according to all that Jehoiada the priest commanded; and they took every man his men, those that were to come in on the sabbath, with those that were to go out on the sabbath, and came to Jehoiada the priest.
10 Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.
And the priest delivered to the captains over hundreds the spear and shields that had been king David's, which were in the house of the LORD.
11 Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.
And the guard stood, every man with his weapons in his hand, from the right side of the house to the left side of the house, along by the altar and the house, by the king round about.
12 Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.”
Then he brought out the king's son, and put upon him the crown and the insignia; and they made him king, and anointed him; and they clapped their hands, and said: 'Long live the king.'
13 Sa’ad da Ataliya ta ji surutun matsara da na mutane, sai ta tafi wurin mutanen a haikalin Ubangiji.
And when Athaliah heard the noise of the guard and of the people, she came to the people into the house of the LORD.
14 Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”
And she looked, and, behold, the king stood on the platform, as the manner was, and the captains and the trumpets by the king; and all the people of the land rejoiced, and blew with trumpets. Then Athaliah rent her clothes, and cried: 'Treason, treason.'
15 Yehohiyada ya umarci komandodin sojoji waɗanda suke lura da mayaƙa, ya ce, “Ku fitar da ita daga cikinku, ku kuma kashe duk wanda ya bi ta.” Gama firist ɗin ya ce, “Kada a kashe ta a cikin haikalin Ubangiji.”
And Jehoiada the priest commanded the captains of hundreds, the officers of the host, and said unto them: 'Have her forth between the ranks; and him that followeth her slay with the sword'; for the priest said: 'Let her not be slain in the house of the LORD.'
16 Saboda haka suka kama ta yayinda ta kai inda dawakai sukan shiga filin fada, a can kuwa aka kashe ta.
So they made way for her; and she went by the way of the horses' entry to the king's house; and there was she slain.
17 Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari tsakanin Ubangiji da sarki da kuma mutane cewa za su zama mutanen Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane.
And Jehoiada made a covenant between the LORD and the king and the people, that they should be the LORD'S people; between the king also and the people.
18 Sai dukan mutanen ƙasar suka tafi haikalin Ba’al suka rushe shi. Suka farfasa bagadai da kuma gumaka, suka kuma kashe Mattan wanda yake firist na Ba’al a gaban bagade. Sa’an nan Yehohiyada firist ya sa matsara a haikalin Ubangiji.
And all the people of the land went to the house of Baal, and broke it down; his altars and his images broke they in pieces thoroughly, and slew Mattan the priest of Baal before the altars. And the priest appointed officers over the house of the LORD.
19 Ya tafi tare da komandodin sojoji, Keretawa, matsara da kuma dukan mutanen ƙasar, tare kuwa suka kawo sarki daga haikalin Ubangiji zuwa cikin fada, ta ƙofar matsara. Sarki kuwa ya ɗauki mazauninsa a bisa kursiyin sarauta,
And he took the captains over hundreds, and the Carites, and the guard, and all the people of the land; and they brought down the king from the house of the LORD, and came by the way of the gate of the guard unto the king's house. And he sat on the throne of the kings.
20 dukan mutanen ƙasar suka yi murna. Birnin ya sami salama don an kashe Ataliya da takobi a fada.
So all the people of the land rejoiced, and the city was quiet; and they slew Athaliah with the sword at the king's house.
21 Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya fara mulki.
Jehoash was seven years old when he began to reign.

< 2 Sarakuna 11 >