< 2 Tarihi 36 >

1 Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a Urushalima yă gāji mahaifinsa.
Then the people of the land took Jehoahaz the son of Josiah, and they anointed him and made him king in his father's place in Jerusalem.
2 Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku.
Joahaz was twenty-three years old when he began to reign; and he reigned three months in Jerusalem.
3 Sarkin Masar ya tumɓuke shi a Urushalima, ya tilasta Yahuda su biya haraji talenti ɗari na azurfa da kuma talentin zinariya.
The king of Egypt deposed him at Jerusalem, and fined the land one hundred talents of silver and a talent of gold.
4 Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwan Yehoyahaz, sarki a bisa Yahuda da kuma Urushalima, ya kuma canja sunan Eliyakim zuwa Yehohiyakim. Amma Neko ya ɗauki Yehoyahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai Masar.
The king of Egypt made Eliakim his brother king over Judah and Jerusalem, and changed his name to Jehoiakim. Neco took Joahaz his brother, and carried him to Egypt.
5 Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa.
Jehoiakim was twenty-five years old when he began to reign; and he reigned eleven years in Jerusalem: and he did that which was evil in the sight of YHWH his God.
6 Nebukadnezzar sarkin Babilon ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya daure da sarƙoƙin tagulla, ya kuma kai shi Babilon.
Against him came up Nebuchadnezzar king of Babylon, and bound him in fetters, to carry him to Babylon.
7 Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kuma kwaso kayayyaki daga haikalin Ubangiji ya sa su a haikalinsa a can.
Nebuchadnezzar also carried of the vessels of the house of YHWH to Babylon, and put them in his temple at Babylon.
8 Sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim, ayyukan banƙyamar da ya aikata da dukan abubuwan da aka same shi da su, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Now the rest of the acts of Jehoiakim, and his abominations which he did, and that which was found in him, look, they are written in the book of the kings of Israel and Judah: and Jehoiachin his son reigned in his place.
9 Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.
Jehoiachin was eighteen years old when he began to reign; and he reigned three months and ten days in Jerusalem: and he did that which was evil in the sight of YHWH.
10 Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima.
At the return of the year king Nebuchadnezzar sent, and brought him to Babylon, with the goodly vessels of the house of YHWH, and made Zedekiah his relative king over Judah and Jerusalem.
11 Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya.
Zedekiah was twenty-one years old when he began to reign; and he reigned eleven years in Jerusalem:
12 Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba.
and he did that which was evil in the sight of YHWH his God; he did not humble himself before Jeremiah the prophet speaking from the mouth of YHWH.
13 Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba.
He also rebelled against king Nebuchadnezzar, who had made him swear by God: but he stiffened his neck, and hardened his heart against turning to YHWH, the God of Israel.
14 Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.
Moreover all the chiefs of the priests, and the people, trespassed very greatly after all the abominations of the nations; and they polluted the house of YHWH which he had made holy in Jerusalem.
15 Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.
YHWH, the God of their fathers, sent to them by his messengers, rising up early and sending, because he had compassion on his people, and on his dwelling place:
16 Amma suka yi wa’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.
but they mocked the messengers of God, and despised his words, and scoffed at his prophets, until the wrath of YHWH arose against his people, until there was no remedy.
17 Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.
Therefore he brought on them the king of the Chaldeans, who killed their young men with the sword in the house of their sanctuary, and had no compassion on young man or virgin, old man or gray-headed: he gave them all into his hand.
18 Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon.
All the vessels of God's house, great and small, and the treasures of the house of YHWH, and the treasures of the king, and of his officials, all these he brought to Babylon.
19 Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can.
They burnt God's house, and broke down the wall of Jerusalem, and burnt all its palaces with fire, and destroyed all the goodly vessels of it.
20 Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa.
He carried those who had escaped from the sword away to Babylon; and they were servants to him and his sons until the reign of the kingdom of Persia:
21 Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.
to fulfill the word of YHWH by the mouth of Jeremiah, until the land had enjoyed its Sabbaths. As long as it lay desolate it kept Sabbath, to fulfill seventy years.
22 Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,
Now in the first year of Koresh king of Persia, that the word of YHWH by the mouth of Jeremiah might be accomplished, YHWH stirred up the spirit of Koresh king of Persia, so that he made a proclamation throughout all his kingdom, and put it also in writing, saying,
23 “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “‘Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’”
"Thus says Koresh king of Persia, 'YHWH, the God of heaven, has given all the kingdoms of the earth to me; and he has commanded me to build him a house in Jerusalem, which is in Judah. Whoever there is among you of all his people, YHWH his God be with him, and let him go up.'"

< 2 Tarihi 36 >