< 1 Tarihi 2 >

1 Waɗannan su ne’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun, 2 Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher. 3 ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi. 4 Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi’ya’ya maza biyar ne. 5 ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul. 6 ’Ya’yan Zera maza su ne, Zimri, Etan, Heman, Kalkol da Darda, su biyar ne. 7 ’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta. 8 Ɗan Etan shi ne, Azariya. 9 ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb. 10 Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda. 11 Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz, 12 Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse. 13 Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya, 14 na huɗun Netanel, na biyar Raddai, 15 na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda. 16 ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel.’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel. 17 Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel. 18 Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon. 19 Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur. 20 Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel. 21 Daga baya, Hezron ya kwana da’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub. 22 Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad. 23 (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad. 24 Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa. 25 ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya. 26 Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam. 27 ’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker. 28 ’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada.’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur. 29 Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid. 30 ’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara. 31 Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai. 32 ’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara. 33 ’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel. 34 Sheshan ba shi da’ya’ya maza, sai’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha. 35 Sheshan ya ba da’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai. 36 Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad, 37 Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed, 38 Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya, 39 Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa, 40 Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum 41 Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama. 42 ’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron. 43 ’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema. 44 Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai. 45 Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur. 46 Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez. 47 ’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af. 48 Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana. 49 Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya.’Yar Kaleb ita ce Aksa. 50 Waɗannan su ne zuriyar Kaleb.’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim, 51 Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader. 52 Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa, 53 kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito. 54 Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa, 55 kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab.

< 1 Tarihi 2 >