< 1 Tarihi 1 >

1 Adamu, Set, Enosh, 2 Kenan, Mahalalel, Yared, 3 Enok, Metusela, Lamek, Nuhu. 4 ’Ya’yan Nuhu maza su ne, Shem, Ham da Yafet. 5 ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras. 6 ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat da Togarma. 7 ’Ya’yan Yaban maza su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim. 8 ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana. 9 ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka.’Ya’yan Ra’ama maza su ne, Sheba da Dedan 10 Kush shi ne mahaifin Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya. 11 Masar shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa, 12 Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa. 13 Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa, 14 Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa 15 Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa, 16 Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa. 17 ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram.’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Meshek. 18 Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuwa shi ne mahaifin Eber. 19 Aka haifa wa Eber’ya’ya maza biyu. Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan. 20 Yoktan shi ne mahaifin Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera 21 Hadoram, Uzal, Dikla, 22 Ebal, Abimayel, Sheba, 23 Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan’ya’yan Yoktan maza ne. 24 Shem, Arfakshad, Shela, 25 Eber, Feleg, Reyu 26 Serug, Nahor, Tera 27 da Abram (wato, Ibrahim). 28 ’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel. 29 Waɗannan su ne zuriyarsu. Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam, 30 Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema 31 Yetur, Nafish da Kedema. Waɗannan su ne’ya’yan Ishmayel maza. 32 ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan. 33 ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura. 34 Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku.’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila. 35 ’Ya’yan Isuwa maza, su ne, Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora 36 ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz, da Timna wanda aka haifa wa Amalek. 37 ’Ya’yan maza Reyuwel su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza. 38 ’Ya’yan Seyir maza su ne, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan. 39 ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ita ce’yar’uwar Lotan. 40 ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam.’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana. 41 Ɗan Ana shi ne, Dishon.’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran. 42 ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan.’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran. 43 Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba. 44 Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki. 45 Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki. 46 Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit. 47 Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki. 48 Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki. 49 Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki. 50 Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel’yar Matired,’yar Me-Zahab. 51 Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet 52 Oholibama, Ela, Finon 53 Kenaz, Teman, Mibzar, 54 Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.

< 1 Tarihi 1 >