< 1 Chronicles 26 >

1 For the divisions of the doorkeepers: of the Korahites, Meshelemiah the son of Kore, of the sons of Asaph.
Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin’ya’yan Asaf maza.
2 Meshelemiah had sons: Zechariah the firstborn, Jediael the second, Zebadiah the third, Jathniel the fourth,
Meshelemiya yana da’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,
3 Elam the fifth, Jehohanan the sixth, and Eliehoenai the seventh.
Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai.
4 Obed-Edom had sons: Shemaiah the firstborn, Jehozabad the second, Joah the third, Sacar the fourth, Nethanel the fifth,
Obed-Edom shi ma yana da’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar,
5 Ammiel the sixth, Issachar the seventh, and Peullethai the eighth; for God blessed him.
Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.)
6 Sons were also born to Shemaiah his son, who ruled over the house of their father; for they were mighty men of valor.
Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.
7 The sons of Shemaiah: Othni, Rephael, Obed, and Elzabad, whose relatives were valiant men, Elihu, and Semachiah.
’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.
8 All these were of the sons of Obed-Edom with their sons and their brothers, able men in strength for the service: sixty-two of Obed-Edom.
Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.
9 Meshelemiah had sons and brothers, eighteen valiant men.
Meshelemiya yana da’ya’ya maza da kuma’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka.
10 Also Hosah, of the children of Merari, had sons: Shimri the chief (for though he was not the firstborn, yet his father made him chief),
Hosa dangin Merari yana da’ya’ya maza. Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari),
11 Hilkiah the second, Tebaliah the third, and Zechariah the fourth. All the sons and brothers of Hosah were thirteen.
Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku sai kuma Zakariya na huɗu.’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka.
12 Of these were the divisions of the doorkeepers, even of the chief men, having offices like their brothers, to minister in the LORD’s house.
Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi.
13 They cast lots, the small as well as the great, according to their fathers’ houses, for every gate.
Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba.
14 The lot eastward fell to Shelemiah. Then for Zechariah his son, a wise counselor, they cast lots; and his lot came out northward.
Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya. Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa.
15 To Obed-Edom southward; and to his sons the storehouse.
Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan’ya’yansa maza.
16 To Shuppim and Hosah westward, by the gate of Shallecheth, at the causeway that goes up, watchman opposite watchman.
Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa. Aikin tsaro bisa ga mai tsaro.
17 Eastward were six Levites, northward four a day, southward four a day, and for the storehouse two and two.
Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu-biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.
18 For Parbar westward, four at the causeway, and two at Parbar.
Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filin kansa.
19 These were the divisions of the doorkeepers; of the sons of the Korahites, and of the sons of Merari.
Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari.
20 Of the Levites, Ahijah was over the treasures of God’s house and over the treasures of the dedicated things.
’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe.
21 The sons of Ladan, the sons of the Gershonites belonging to Ladan, the heads of the fathers’ households belonging to Ladan the Gershonite: Jehieli.
Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli,
22 The sons of Jehieli: Zetham, and Joel his brother, over the treasures of the LORD’s house.
’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. Su ne suke kula da ma’ajin haikalin Ubangiji.
23 Of the Amramites, of the Izharites, of the Hebronites, of the Uzzielites:
Daga zuriyar Amram, Izhar, mutanen Hebron da kuma Uzziyel, su ma aka ba su aiki.
24 Shebuel the son of Gershom, the son of Moses, was ruler over the treasuries.
Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’i mai lura da baitulmali.
25 His brothers: of Eliezer, Rehabiah his son, and Jeshaiah his son, and Joram his son, and Zichri his son, and Shelomoth his son.
Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit.
26 This Shelomoth and his brothers were over all the treasuries of the dedicated things, which David the king, and the heads of the fathers’ households, the captains over thousands and hundreds, and the captains of the army, had dedicated.
Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.
27 They dedicated some of the plunder won in battles to repair the LORD’s house.
Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji.
28 All that Samuel the seer, Saul the son of Kish, Abner the son of Ner, and Joab the son of Zeruiah had dedicated, whoever had dedicated anything, it was under the hand of Shelomoth and of his brothers.
Shelomit da’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.
29 Of the Izharites, Chenaniah and his sons were appointed to the outward business over Israel, for officers and judges.
Daga mutanen Izhar, Kenaniya da’ya’yansa maza su aka sa a ayyukan da ba na haikali ba, su suka zama manya da kuma alƙalai a bisa Isra’ila.
30 Of the Hebronites, Hashabiah and his brothers, one thousand seven hundred men of valor, had the oversight of Israel beyond the Jordan westward, for all the business of the LORD and for the service of the king.
Daga zuriyar Hebron, Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki.
31 Of the Hebronites, Jerijah was the chief of the Hebronites, according to their generations by fathers’ households. They were sought for in the fortieth year of the reign of David, and mighty men of valor were found among them at Jazer of Gilead.
Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne.
32 His relatives, men of valor, were two thousand seven hundred, heads of fathers’ households, whom King David made overseers over the Reubenites, the Gadites, and the half-tribe of the Manassites, for every matter pertaining to God and for the affairs of the king.
Yeriya yana da’yan’uwa guda dubu biyu da ɗari bakwai, jarumawa da kuma kawunan iyalai, sai Sarki Dawuda ya sa su lura da mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse game da kome da ya shafi Allah da kuma al’amuran sarki.

< 1 Chronicles 26 >