< Revelation 18 >

1 After these things, I saw another angel coming down out of the sky, having great authority. The earth was illuminated with his glory.
Bayan wadannan abubuwa sai na ga wani mala'ika yana saukowa daga sama. Yana da babban iko sosai, duniya kuwa ta haskaka da daukakarsa.
2 He cried with a mighty voice, saying, “Fallen, fallen is Babylon the great, and she has become a habitation of demons, a prison of every unclean spirit, and a prison of every unclean and hated bird!
Ya yi kira da kakkarfar murya cewa, “Ta fadi, Babila mai girma ta fadi! Ta zama mazaunin aljannu, da matattarar kowanne kazamin ruhu da kuma mazaunin kowanne kazami da kyamataccen tsuntsu.
3 For all the nations have drunk of the wine of the wrath of her sexual immorality, the kings of the earth committed sexual immorality with her, and the merchants of the earth grew rich from the abundance of her luxury.”
Gama dukan al'ummai sun sha ruwan innabin fasikancinta. Sarakunan duniya sun aikata fasikanci da ita. Attajiran duniya sun arzuta da ikon rayuwar annashuwarta.”
4 I heard another voice from heaven, saying, “Come out of her, my people, that you have no participation in her sins, and that you don’t receive of her plagues,
Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fito daga cikinta, mutanena, domin kada kuyi zunubi irin na ta, domin kuma kada bala'inta ya auko maku.
5 for her sins have reached to the sky, and God has remembered her iniquities.
Zunubanta sun taru sun yi tsayi har sama. Allah kuma ya tuna da miyagun ayyukanta.
6 Return to her just as she returned, and repay her double as she did, and according to her works. In the cup which she mixed, mix to her double.
Ku saka mata gwargwadon yadda ta saka wa wadansu, ku biya ta ninki biyu na abin da ta yi; a cikin kokon da ta dama, ku dama mata ninki biyu.
7 However much she glorified herself and grew wanton, so much give her of torment and mourning. For she says in her heart, ‘I sit a queen, and am no widow, and will in no way see mourning.’
Kamar yadda ta daukaka kanta ta yi ta annashuwa, ku wahalsheta da azaba da bakin ciki haka. Domin ta ce a zuciyarta, 'Ina zaune kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taba yin makoki ba,'
8 Therefore in one day her plagues will come: death, mourning, and famine; and she will be utterly burned with fire, for the Lord God who has judged her is strong.
Saboda haka a rana daya bala'inta zai auko mata; mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta za ta kona ta kurmus, domin Ubangiji Allah mai iko ne, kuma shine mai hukuntata.”
9 The kings of the earth who committed sexual immorality and lived wantonly with her will weep and wail over her, when they look at the smoke of her burning,
Sarakunan duniya da suka yi fasikanci, har suka baude tare da ita, za su yi kuka da kururuwa domin ta sa'adda suka ga hayakin kunarta.
10 standing far away for the fear of her torment, saying, ‘Woe, woe, the great city, Babylon, the strong city! For your judgment has come in one hour.’
Za su tsaya can nesa suna tsoron azabarta, suna cewa, “Kaito, kaiton babban birni, Babila, birni mai iko! Domin cikin sa'a guda hukuncinta ya zo.”
11 The merchants of the earth weep and mourn over her, for no one buys their merchandise any more:
Manyan 'yan kasuwan duniya za su yi kuka da bakin ciki dominta, da shike ba wanda ke sayan kayanta kuma -
12 merchandise of gold, silver, precious stones, pearls, fine linen, purple, silk, scarlet, all expensive wood, every vessel of ivory, every vessel made of most precious wood, and of brass, and iron, and marble;
kayan zinariya, azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'u-lu'u, da lilin mai laushi, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jar alharini da itacen kamshi iri iri, da kayan da aka sassaka da itace mai tsada, da na tagulla, da na bakin karfe, da na dutse mai sheki,
13 and cinnamon, incense, perfume, frankincense, wine, olive oil, fine flour, wheat, cattle, sheep, horses, chariots, and people’s bodies and souls.
da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur da lubban, da ruwan innabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawakai, da kekunan doki, da bayi, da rayukan 'yan adam.
14 The fruits which your soul lusted after have been lost to you. All things that were dainty and sumptuous have perished from you, and you will find them no more at all.
Amfanin da kika kwallafa rai da duk karfinki sun fice daga gareki. Duk annashuwarki da darajarki sun bace, ba za a kara samunsu ba kuma.
15 The merchants of these things, who were made rich by her, will stand far away for the fear of her torment, weeping and mourning,
Manyan 'yan kasuwa na wadannan kaya da suka azurta ta wurinta, za su tsaya can nesa da ita, sabili da tsoron azabarta, kuka da kururuwar bakin ciki.
16 saying, ‘Woe, woe, the great city, she who was dressed in fine linen, purple, and scarlet, and decked with gold and precious stones and pearls!
Za su ce, “Kaito, kaito ga babban birni da take sanye da lilin mai laushi da tufafi masu jar garura da kuma jan alharini, da ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsu masu daraja da lu'u-lu'u!
17 For in an hour such great riches are made desolate.’ Every ship master, and everyone who sails anywhere, and mariners, and as many as gain their living by sea, stood far away,
A cikin sa'a guda duk dukiyan nan ta lallace. Kowanne matukin jirgin ruwa, da fasinjoji, da masu tuki da duk wadanda suke samun biyan bukatun rayuwarsu daga ruwa, suka tsaya can nesa.
18 and cried out as they looked at the smoke of her burning, saying, ‘What is like the great city?’
Suka yi kuka sa'anda suka ga hayakin kunarta. Suka ce, “Wanne birni ne ya yi kama da babban birnin?”
19 They cast dust on their heads, and cried, weeping and mourning, saying, ‘Woe, woe, the great city, in which all who had their ships in the sea were made rich by reason of her great wealth!’ For she is made desolate in one hour.
Suka watsa kura a kawunansu, suka yi kuka da karfi, da kururuwa da bakin ciki, “Kaito, kaiton babban birnin nan inda duk masu jiragen ruwa suka azurta daga dukiyarta. Domin a sa'a guda an hallakar da ita.”
20 “Rejoice over her, O heaven, you saints, apostles, and prophets, for God has judged your judgment on her.”
“Ku yi murna a kanta, sama, ku masu ba da gaskiya, manzanni, da annabawa, domin Allah ya kawo hukuncinku a kanta!”
21 A mighty angel took up a stone like a great millstone and cast it into the sea, saying, “Thus with violence will Babylon, the great city, be thrown down, and will be found no more at all.
Wani kakkarfan mala'ika ya dauki wani dutse mai kama da dutsen nika, ya jefa shi cikin teku yana cewa, “Ta wannan hanya, Babila, babban birnin, za a jefar da ita kasa da karfi, ba za a kara ganinsa ba.
22 The voice of harpists, minstrels, flute players, and trumpeters will be heard no more at all in you. No craftsman of whatever craft will be found any more at all in you. The sound of a mill will be heard no more at all in you.
Muryar masu kidar molaye, mawaka, masu busa sarewa, da na masu busa algaita, ba za a kara ji a cikinta ba. Babu wani mai kowanne irin sana'a da za a samu a cikinta. Ba za a kara jin karar nika a cikinta ba.
23 The light of a lamp will shine no more at all in you. The voice of the bridegroom and of the bride will be heard no more at all in you, for your merchants were the princes of the earth; for with your sorcery all the nations were deceived.
Hasken fitila ba za ya kara haskakawa a cikin ki ba. Ba za a kara jin muryoyin ango da na amarya a cikinki ba, domin attajiranki sune 'ya'yan masu mulki a duniya, kuma ta wurin sihirinki kika yaudari al'ummai.
24 In her was found the blood of prophets and of saints, and of all who have been slain on the earth.”
A cikinta aka sami jinin annabawa da na masu ba da gaskiya, da jinin duk wadanda aka kashe a duniya.”

< Revelation 18 >